| Hausa
SIYASA
2 minti karatu
Jam’iyyar PDP ɓangaren Kabiru Turaki ta ɗage zaman kwamitin gudanarwarta na farko saboda hargitsi
Rahotanni sun ce an samu yamutsi a hedikwatar jam'iyyar a babban birnin Nijeriya Abuja, kafin Turaki ya yi jawabi ga manema labarai.
Jam’iyyar PDP ɓangaren Kabiru Turaki ta ɗage zaman kwamitin gudanarwarta na farko saboda hargitsi
kabiru Tanimu Turaki ya taɓa minista na yyuka na mausamman a lokacin mulkin Shugaban Goodluck Jonathan / Getty Images
18 Nuwamba 2025

Kabiru Turaki, Shugaban jam’iyyar PDP mai adawa a Nijeriya ya ce jam’iyyar ta ɗaga zaman farko na kwamitin gudawarwarta wanda ta shirya yi ranar talata a Abuja.

Da yake magana da manema labarai bayan ya samu shiga cikin hedikwatar jam’iyyar a ginin Wadata Plaza, Turaki ya ce an ɗauki wannan matakin ne sakamakon “ayyukan masu yi wa Dimokuraɗiyya karan-tsaye”.

Ya ce yanzu za a yi zaman ne ranar Laraba 19 ga watan Nuwamba.

Turaki, wanda yake tare da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, da gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed, ya yaba wa kwamishinan ‘yan sandan Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja, saboda irin tsaron da ya bai wa shugabannin jam’iyyar, har suka samu damar shiga hedikwatarta.

Ya ce shi ya yi wa kwamishinan bayani game da shirin kwamitin gudanawar jam’iyyar da aka shirya yi da kuma “takardun da suke yawo a shafukan sada zumunta” da ke shelar zaman kwamitin zartarwa da kwamitin amitattu na wasu mutane da tuni suka bar jam’iyyar.

Ya ce ‘yan sanda sun cika alƙawarinsu wajen tabbatar da cewa shugabannin jam’iiyar sun iya shiga harabar domin yi wa manema labarai jawabi.

Turaki ya gode wa masu ruwa da tsaki bisa goyon bayanusu, yana mai cewa jam’iyyar PDP ta amice wajen tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya.

Ya ce gwamnonin da ‘yan majalisar dokokin ƙasa da tsofaffin gwamnoni da tsofaffin ministoci da kuma waɗanda suka bar kwamitin amittatun jam’iyyar kwanan nan sun nuna haɗin kai, inda suka raka shi hedikwatar jam’iyyar.

Ya ce PDP ta mayar da hankalinta kan dawo da ƙarfinta, kuma dole ta fara tabbatar da haɗin kai a faɗin ƙasar kafin ta iya komawa mulki.

Ɗage zaman na zuwa ne yayin da ake rikicin shugabancin da ya raba jam’iyyar gida biyu, inda ɓangaren Turaki ke jaddada dacewarsa bayan ya kori Samuel Anyanwu, tsohon sakataren jam’iyar.

Rumbun Labarai
Yadda 'nadamar zalunci' ke janyo rushewar lafiyar ƙwaƙwalwa a rundunar sojin Isra’ila
Me ya sa Trump da masu sharhi da ke da ra’ayin rikau ke sa ido kan al’ummar Somalia da ke Minnesota?
Shugaban Nijar Tiani ya karɓi shugaban Bilma bayan ya yi watanni 16 a hannun masu garkuwa da mutane
An daƙile harin RSF kan West Kordofan: Rundunar Sojin Sudan
Nijar ta ce ta fara kai uranium ɗinta kasuwar duniya
Trump ya ce Amurka za ta dakatar da hijirar 'yan cirani daga kasashe marasa arziki har abada
Gobarar Hong Kong: Adadin waɗanda suka mutu ya kai 128 yayin da aka shiga kwana uku a ƙoƙarin ceto
China ta yi gargaɗin 'murƙushe' katsalandan ɗin ƙetare kan shirin makami mai linzani na Japan
Yaƙin Sudan: Maye gurbin UAE da Turkiyya na iya ƙarfafa ƙoƙarin ƙasashe na samar da zaman lafiya
Yadda muhawarar Kyamar Musulunci a Birtaniya ta fito da munafurcin kasar
Ta yaya barazanar Trump ga Nijeriya za ta yi tasiri kan siyasar Yammacin Afirka mai rauni?
Daga Baghdad zuwa Abuja: Tsohon tuggun Amurka da sunan ‘yanci da mamaya
Yadda wata sabuwar doka a India za ta cutar da Musulmai da sunan yaki da ‘Auren Jihadi’
Shugabar ƙasar Tanzania Samia Hassan ta sha rantsuwar kama aiki a wa’adi na biyu
Kutungwilar Netanyahu kan tsagaita wuta a Gaza ita ce ci gaba da kashe Falasdinawa
Zaben Tanzania: Intanet ya katse sannan zanga-zanga ta barke a ranar zabe
Masu nazarin kayan tarihi sun gano kisan gillar Faransa a wata makabartar Senegal
Mahama ya hana ministoci bayyana manufofin gwamnatin Ghana sai da izinin majalisar ministoci
Shugaban Sudan al Burhan ya ce ‘sojojin ƙasar sun janye’ daga Al Fasher
Hamas na aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta amma Isra'ila na ci gaba da karya ta, in ji Erdogan