Mahaucin Al Fasher: Yadda hotonsa ya zama alamar bakin cikin Sudan
AFIRKA
7 minti karatu
Mahaucin Al Fasher: Yadda hotonsa ya zama alamar bakin cikin Sudan“Mahaucin Al Fasher” ya zama alamar aikata muggan laifuka ga bil’adama a Sudan, wanda ke bayyana yadda yakin RSF da sojoji ya koma rikicin ‘yan bindiga a yayin da duniya ke kallo daga gefe guda.
Abu Lulu wanda asalin sunansa Al Fatah Abdullah Idris na daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar RSF mafiya hatsari.
kwana ɗaya baya

Gawarwaki a kan tituna. Fararen hula suna neman rahama. 'Yan bindiga suna harbin mutane ba tare da wata shakka ba.

Halin da garin Al Fasher ke ciki ke nan a yanzu, bayan da rundunar mayakan RSF suka kwace babban birnin Jihar Darfur ta Arewa da ke yammacin Sudan kwanan nan.

"Birnin ya koma budaddiyar makabarta," in ji Sulaiman Sharif, daraktan sashen yaki da cin zarafin mata a gwamnatin rikon kwarya ta Sudan.

Daga cikin masu aikata wannan ta'asa da yawa, wani suna ya zama kamar zaluncin zamanin farko: Abu Lulu, wanda aka fi sani da "Mahaucin Al Fasher".

Wani bidiyon TikTok da aka riga aka cire daga manhajar tuntuni ya nuna Lulu yana alfahari da cewa ya kashe mutane kusan 2,000 da kansa.

A wani bidiyon, an ga mai kisan gillar na magana da wasu mutane kafin ya harbe su daya bayan daya a wani wuri.

Akwai wani bidiyo na uku inda yake ɗaukar hoto da waɗanda abin ya shafa. Bayan 'yan daƙiƙa kaɗan, sai ya harba musu harsashai.

Haka nan ya yi mu'amala da wani mutum da da aka ji wa rauni, kafin harbin bindiga ya maye gurbin tattaunawar tasu ta ɗan gajeren lokaci.

"Yana alfahari da abin da yake yi, kuma yana ajiye ayyukansa ta hanyar da ke nuna cewa yana yin aiki mai kyau," in ji masanin tarihi na Sudan Tarig Mohamed Nour yayin tattaunawa da TRT Afrika.

Lulu, wanda ake cewa ainihin sunansa shi ne Al-Fateh Abdullah Idris, ya sami shuhura cikin sauri a matsayin kwamandan 'yan bindiga mafi iya zalunci a kungiyar mayakan RSF.

An ruwaito cewa ya shiga ƙungiyar mayakan a shekarar 2013 kuma ya girma cikin sauri inda ya zama ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan da ke da hannu a rikicin da ke faruwa a Sudan.

Zalunci marar yankewa

Yaƙin basasa tsakanin RSF da Sojojin Sudan ya ɓarke ​​a Khartoum a watan Afrilun 2023, wanda ya ƙara tsananta yaƙin da ake yi bayan hambarar da tsohon Shugaban Kasa Omar al-Bashir a shekarar 2019.

A farkon wannan watan, mayakan RSF sun kama garin Al Fasher bayan sun kewaye sansanin sojojin Sudan na ƙarshe a yankin Darfur na yammacin ƙasar na tsawon watanni 18.

Abin da ya biyo baya shi ne ta'addanci da ya bayyana karara inda har aka ga kisan gillar Al Fasher daga sararin samaniya ta tauraron dan’adam.

"Abin da ke faruwa a Al Fasher ya zama laifukan cin zarafin bil'adama. An kashe mutane, an lalata gidaje, kuma an raba iyalai da junansu.

“Duniya tana kallo, amma babu wanda ke hana faruwar hakan," in ji Dr Tunç Demirtaş, malami a sashen nazarin alakar kasa da kasa a Jami’ar da ke Turkiyya.

"Abin da RSF ke yi a Al Fasher shi ne kawar da wata ƙabila. A bayyane yake karara cewa dokokin ƙasa da ƙasa suna wanzuwa ne kawai a baki ko a rubuce.

“'Yan bindiga kamar RSF suna samun ƙarfin gwiwa sakamakon hakan; sun san babu wani sakamako da zai biyo bayan ta’annatin da suke yi."

Lasisin aikata kisan gilla

Kamfanin Dillancin Labarai na Anadolu ya rawaito cewa Lulu ya zama ɗaya daga cikin amintattun masu gadin Abdul Raheem Dagalo, ɗan'uwan shugaban RSF Mohammed Hamdan Dagalo - wanda mabiyansa ke yi wa lakabi da Hemedti - bayan barkewar rikici mai tsanani a shekarar 2023.

Ya kasance a sahun gaba a ta'addancin 'yan bindiga a faɗin Sudan tun daga lokacin, kodayake kwace iko da Al Fasher ya ɗauki lokaci kafin ya nuna sha'awarsa ta zalunci ba tare da nadama ba.

"Ɗaya ne cikin biyu, ko dai ya yi nasara ko kuma ya mutu," in ji Lulu a wani bidiyo yayin da sauran 'yan bindiga da ke kewaye da shi yana dariya.

Nour ya yi imanin cewa "Mahaucin Al Fasher" yana ɓoye gaskiyar abin da ake kira a wani mataki da ba za a iya misaltawa ba.

"Abu Lulu ya bayyana cewa ya kashe mutane 2,000 da hannunsa... Nawa ne sauran mutanen da ke kewaye da shi suka kashe?" yana mamaki.

Tarihin zubar da jini a Darfur

Rundunar RSF ta bulla a shekarar 2013 daga gyauron 'yan tawayen Janjaweed, waɗanda tsohon Shugaba al-Bashir ya wakilta don murkushe wani tawaye a yankin Darfur. A cewar Majalisar Dinkin Duniya, akalla mutane 180,000 aka kashe a lokacin.

"Muna sake shaida abin da ya faru a Darfur a shekarar 2003," in ji masanin tarihi Nour a tattaunawa da TRT Afrika.

Kwanaki bayan kisan gillar da aka yi a Al Fasher, kwamandan RSF Hemedti ya amince da take dokoki da sojojinsa suka yi kuma ya yi alƙawarin gudanar da bincike. Lulu yana cikin waɗanda ƙungiyar ta "kama", amma bai dade a tsare ba.

"Sun tsare shi na tsawon kwana biyu ko uku sannan shugaban ƙabilun ya zo ya ce, 'Ya'yanmu sun yi yaƙi a kanku sannan kun saka su a gidan yari'.

“Don haka, mun saka Abdul Raheem Dagalo yana neman a saki wannan mahauci tare da ba shi saƙo bayyananne: kada a dauki hoto da bidiyon abin da kuka yi," in ji Nour.

Tsararren shiri

Mutane da yawa na kallon daurin na ɗan gajeren lokaci da aka yi wa Lulu a matsayin wata dabarar da RSF ta yi don wanke tsarinta na shugabanci daga duk wani laifi da ya faru a wannan kisan gillar.

"Yanzu, suna ƙoƙarin cewa waɗannan bidiyon mutum ɗaya ne ya yi su, ko kuma suna ƙoƙarin nuna cewa wannan mutum ɗaya ne kawai ke aikata waɗannan laifukan," in ji Sharif.

A yanzu mayakan RSF na iko da dukkan jihohi biyar na yankin Darfur, inda birnin Al Fasher mai mahimmanci ya zama katangar ƙarshe da ta faɗi.

"Darfur na nufin ƙasar Fur, Zaghawa, Tunjur da sauran ƙabilun Afirka. Yanzu, 'yan bindiga suna murnar cewa Darfur zai zama Dar na sauran al'ummomi kamar ƙabilun Larabawa," in ji Sharif a tattaunawa da TRT Afrika.

Demirtaş ya bayyana damuwa da rashin shiga tsakani na ƙasashen duniya ko da bayan an rasa rayuka da yawa. "Tambayar ita ce ba wai ko duniya za ta iya daukar mataki ba ce, a’a shin tana son yin hakan.

“Akwai tsananin rashin bayyana niyya. Kuma ba tare da aniyar shugabanci ba, babu wata hukuma da za ta iya kare ‘yan baruwana,” in ji shi.

Har yanzu ba a san ko za a gurfanar da Lulu da sauran 'yan bindigar RSF a gaban kuliya ba, kodayake Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta amince cewa ta'asar da aka yi a Al Fasher ta kai ga laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil'adama.

A ranar 6 ga Nuwamba RSF ta sanar da cewa ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta jinkai da wata kungiyar masu shiga tsakani da Amurka ke jagoranta ta gabatar.

Amma rundunar sojin Sudan ta dage cewa za ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ne kawai idan RSF ta janye daga yankunan fararen hula, kuma ta ajiye makamai.

"Abin da muke gani a Al Fasher a yau wata sabuwar Gaza ce," Demirtaş ya fada wa TRT Afrika. "Tsarin duniya na yanzu ya lalace. Bala'i ne ga bil'adama."

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa mutane 82,000 daga cikin al'ummar Al Fasher su 260,000 sun tsere daga gidajensu don guje wa kashe su, azabtar da su ko kuma tsananta musu da mayakan RSF ke yi. Da yawa har yanzu na cikin tasku. Mummunan bala'in jinkai na duniya ne da ke ta’azzara.

Rumbun Labarai
UN Women: Mata da 'yan mata 11M suna fama da matsanancin ƙarancin abinci a Sudan sakamakon yaƙi
WHO ta bayyana damuwa kan karuwar masu ciwon siga a Afirka
Kisan kare dangi a boye da bayyane: Gushewar jinkai a Al Fasher
An ba da belin dan Gaddafi bayan da ya shafe shekaru 10 a tsare a Lebanon
Gwamnatin Trump 'ta aika wa Equatorial Guinea dala miliyan 7.5' don ta karɓi waɗanda Amurka ta kora
Ƙasashe fiye da 20 sun yi Allah wadai da RSF kan kashe-kashen da take yi a Sudan
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi kira da a dakatar da zubar da jini a Sudan
Paul Biya na Kamaru: Dan siyasar da zai ci gaba da yin mulki har sai ya kai shekara 99?
Hare-haren RSF sun kori ƙarin dubban mutane daga Darfur da Kordofan na Sudan
RSF ta binne gawawwaki a kabarin bai-ɗaya, ta ƙone wasu domin 'ɓoye laifukan yaƙi': Likitocin Sudan
Sojojin Sudan sun harbo jirgi maras matuƙi na RSF a Kordofan ta Arewa
Dakarun Nijar sun cafke muggan makamai da aka yi safararsu daga Libya, sun kama masu safarar ƙwayoyi
RSF ta Sudan ta kai hare-hare a Jihar Khartoum da birnin Atbara bayan amincewa da tsagaita wuta
Paul Biya na Kamaru: Shugaban da ya fi tsufa a duniya ya sha rantsuwar kama aiki karo na takwas
Hatsarin mota ya yi ajalin fiye da mutum 1,000 a Nijar a shekarar 2023, fiye da 12,000 sun jikkata
Sabbin hotunan tauraron dan'adam sun gano alamun 'kaburburan bai-daya a El-Fasher a Sudan
MDD ta yi gargaɗin cewa yaƙin Sudan na gurgunta tattalin arzikin Sudan ta Kudu
Trump ya ce bai kamata Afirka ta Kudu ta kasance cikin G20 ba, ba zai je taronta a Johannesburg ba
'Yan Sudan sun ba da mummunan labarin yi wa mata fyade yayin da suke tserewa daga Al Fasher
An kashe mutane 40 a harin da aka kai wa taron jana'iza a yankin Kordofan na Sudan: MDD