Ga mafiya yawan 'yan Uganda, Yoweri Museveni shi kaɗai ne shugaban ƙasa da suka san yana kan mulki tun bayan da ya samu wa'adi na bakwai a zaben da aka kammala kwanan nan.
Kwamitin Zabe ya ce ya samu kaso 71.65 cikin dari na kuri'u, kuma jam'iyyarsa mai mulki ta National Resistance Movement (NRM), ana sa ran za ta ƙara ƙarfafa rinjayenta a majalisar dokoki. 'Yan adawa sun yi watsi da sakamakon inda suka kira shi na "ƙarya".
Shugaban mai shekaru 81 — wanda ya karɓi iko a 1986 bayan jagorantar tawaye na sojoji — yana cikin shugabannin duniya waɗanda suka fi daɗewa a kan mulki a duniya kuma shi ne na uku a sahun shugabannin Afirka da suka dade a kan mulki.
Masu goyon bayansa suna kallon shekarun mulkinsa na shekara 40 a matsayin wani lokaci na zaman lafiya a cikin gida yayin da makwabtansu suka fada cikin rikici. Tun bayan samun 'yancin kan su daga Biritaniya a 1962, Uganda ta sha fama da juyin mulki — an tsige shugabanni tara a cikin shekaru 22 — har sai da Museveni ya hau mulki.
Tsare nasarori
Don neman wa'adi na bakwai, tsohon jagoran ya yi kamfe kan tabbatar wa da nasarorin mulkinsa kuma ya yi alkawarin kai ƙasar zuwa ƙasar da ke samun matsaƙaitan kuɗaɗen shiga.
Ƙasar na dab da samun yalwar arzikin man fetur a yayin da babban kamfanin mai na Faransa, TotalEnergies, da kamfanin mai na kasar Sin mai suna China National Offshore Oil Corporation (CNOOC) ke shirin fara hakar mai a watan Oktoba.
Masana suna cewa dorewar Museveni a mulki ya samo asali ne daga matsayinsa a fagen siyasar duniya da kuma ƙarfi da gwamnati ke da shi wajen sarrafa harkoki a ƙasa.
Ya taimaka ta hanyar aika sojoji zuwa ayyukan wanzar da zaman lafiya na yanki kuma an yaba masa saboda karɓar mafi girman sansanonin 'yan gudun hijira a duniya.
"Yana da goyon bayan yammacin duniya saboda yana kula da bukatunsu a yankin," in ji mai fafutukar hakkin dan’dam na Uganda Kiiza Eron a tattaunawarsa da TRT Afrika.
"Kuma ko da akwai zaman lafiya, wannan zaman lafiyar na dogara ne ga mutum ɗaya."
Akwai damuwa kan 'yancin cibiyoyin gwamnati da kuma rawar da 'yan uwa na shugaban ƙasa ke takawa a gwamnati.
Matarsa ta kasance ministar ilimi a majalisar ministocin da ta gabata, babban ɗansa Janar Muhoozi Kainerugaba, shi ne shugaban sojoji, yayin da wanda suke uba ɗaya, Salim Saleh, shi ne mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin soja.
Masu nazari sun ce 'yan adawa sun kasa karawa da Museveni a tsawon shekaru, suna danganta hakan da rashin juriyar adawa daga gwamnati wanda hakan ya yi ta janyo murkushe 'yan hamayya, duk da cewa hukumomi sun ce matakan an ɗauke su ne don dawo da oda.
Irin waɗannan damuwar ma hukumar kare haƙƙin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta nuna a gabannin zaɓe, inda ta yi Allah wadai da “yawan kame, da tsare jama’a da kuma amfani da ƙarfin da bai kamata ba a kan ‘yan adawa”.
Abokin hamayyarsa na dogon lokaci Kiiza Besigye yana tsare tun Nuwamban 2024 kan zargin cin amanar ƙasa, wanda ke ɗauke da hukuncin kisa. Sai dai ya musanta tuhumar da ake yi masa.
Babban abokin adawar Museveni a zaben makon da ya gabata, Bobi Wine, wanda sunansa na asali Robert Kyagulanyi, ya shiga ɓuya bayan ya ƙalubalanci sahihancin sakamakon.
Hukumar Zabe ta Uganda ba ta mayar da martani kan wannan koke ba, amma a ranar Talata ɗan shugaban ƙasa ya yi barazanar kashe Bobi Wine a shafin X a rubuce-rubucen da daga baya aka goge.
Siyasar duniya da buri
Duk da haka Museveni ya nemi gabatar da dogon lokacin mulkinsa a matsayin abin da yanayi a ƙasar da siyasar duniya suka tilasta, ba buri na kansa ba. Taken kamfen dinsa sun haɗa da ƙarfafa ruhin kishin haɗin-kan Afirka don ganin Uganda da ƙasashen Afirka suna da matsayi mai ƙarfi a tsarin duniya.
Ya ambaci yadda aikin soja na Amurka a Venezuela kwanan nan ya zama "kiran faɗakarwa ga shugabanci mai ƙarfin gwiwa a Afirka" wanda zai ba da fifiko ga tsaron dabarun nahiyar a ƙasa, teku, iska da sarari.
Shugaban mai shekaru 81 yana jagorantar ƙasa mai matasa da yawa — fiye da kaso 73 na mutum miliyan 46 na ƙasar suna ƙasa da shekaru 30, in ji hukumar ƙididdiga ta Uganda. A lokuta da dama a jawabansa yana kiran matasa "‘yayana da jikokina".
Rashin aikin yi tsakanin matasa da yadda ake ganin an ware su daga siyasa sun kasance daga cikin manyan damuwa a zaben.
"Tun daga haihuwata na gan shi (a matsayin shugaban ƙasa). Ya kasance a mulki haka tsawon lokaci saboda dabarunsa," in ji Sultan Ahmed Ikonge a tattaunawarsa da TRT Afrika.















