Kwamitin Gyaran Kundin Tsarin Mulki a Ghana ya bayar da shawarar ƙara wa’adin mulkin shugaban ƙasa zuwa shekara biyar maimakon shekara huɗu wanda ba ya bai wa gwamnatoci damar aiwatar da tsare-tsarensu na kawo ci-gaba.
Da yake gabatar da rahotonsa ga Shugaba John Dramani Mahama a ranar Litinin 22 ga Disamban 2025, a Fadar Shugaban Ƙasa, shugaban kwamitin Farfesa Henry Kwasi Pempeh ya ce sun ɗauki matakin ne da manufar inganta ayyukan gwamnatoci da kuma kawar da batun wa’adin mulki na uku.
“Ba mu bayar da shawarar yin wa’adi na uku ba, babu wanda yake goyon bayan wa’adi na uku, har ma shugaba Mahama da kansa,” in ji shi.
Kwamitin ya kuma lura da cewa wa’adin shekaru huɗu na shugaban ƙasa na ƙarewa ne wajen sake miƙa mulki da harkokin zaɓe a ƙasar.

Farfesa Pempeh ya kuma bayyana cewa “Shugaban Ƙasa na kwashe tsawon watanni shida kafin ya gama zama a ofis, sannan yana kwashe tsawon shekara guda yana kamfe.”
Domin magance hakan, kwamitin ya bayar da shawarar tsara yadda za a gudanar da gangamin zaɓuka domin rage ayyukan siyasa, tare da bai wa gwamnatoci damar yin ayyuka sosai.
An ɗora wa kwamitin alhakin yin nazari ga kwaskwarimar da aka yi wa kundin tsarin mulki a shekarar 2010 da kuma a 2023 tare da warware ƙalubalen da ke tattare da su.
Rahoton da aka tattara tsawon watanni da dama, ya bayar da shawarwarin yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin Ghana na 1992 domin ƙarfafa shugabanci, haɓaka shigar ‘yan ƙasa harkokin gudanarwa da magance muhimman batutuwa na ƙasa.
A yanzu dai, ana jiran matakin da shugaban ƙasa zai ɗauka na aiwatar da shawarwarin, wanda hakan zai zama wani babban mataki a sha’anin mulki da siyasa a Ghana.


















