| Hausa
DUNIYA
4 minti karatu
Martanin duniya na karuwa kan hare-haren da Amurka ta kai wa Venezuela
Jagorori na duniya da 'yanmajalisar Amurka da na Birtaniya da Rasha da Tarayyar Turai suka nuna damuwa kan gagaruman hare-hare na soja sannan sun yi gargadin rikicewar lamarin da tasirinsa kan fararen hula.
Martanin duniya na karuwa kan hare-haren da Amurka ta kai wa Venezuela
US President Donald Trump has announced that American forces carried out a “large-scale strike” against Venezuela. / AFP
3 Janairu 2026

Rubdugun suka daga kasashen duniya sun biyo bayan harin soji na Amurka kan Venezuela, inda shugabanni da 'yanmajalisa a fadin Amurka da Turai suka yi gargaɗi cewa harin ya saba dokar kasa da kasa kuma na iya haifar da karin rashin zaman lafiya.

Shugaban Amurka Donald Trump ya fada da safiyar Asabar cewa rundunar sojin Amurka ta kai "wani babbar hari" kan Venezuela, yana ikirarin an kama shugaban kasa Nicolas Maduro da matarsa aka kuma fitar da su daga kasar.

Wannan sanarwa ta janyo martani mai karfi daga gwamnatocin yankin, da manyan kasashen duniya, da 'yanmajalisar Amurka.

"Haramtaccen harin Amurka"

Shugaban Cuba Miguel Díaz-Canel ya yi Allah-wadai da harin a matsayin "haramtaccen hari na Amurka", yana kiran da duniya ta mayar da martani cikin gaggawa.

"Ana kai wa yankinmu mummunan farmaki," in ji shi a wani sako da ya wallafa a shafin X, yana bayyana aikin a matsayin "ta'addancin gwamnati kan jaruman mutanen Venezuela da kuma kan Amurkanmu."

Masu AlakaTRT Afrika - Ƙarar bamabamai ta rikita birnin Caracas bayan Trump ya sha alwashin kai hari a ƙasar Venezuela

Ministan Harkokin Wajen Cuba Bruno Rodriguez ya kara karfafa wannan suka, yana kiran harin "dabbanci ne kan kasa wadda ba ta kai hari ga Amurka ko wata kasa ba."

Shugaban Kolombiya Gustavo Petro ya yi watsi da "kowane matakin soja da wata ƙasa ta yi gaban kanta da zai kara tabarbara halin da ake ciki ko ya sanya fararen hula cikin haɗari."

A wata sanarwa daban, Petro ya ce ya kira taron kwamitin tsaro na ƙasa kuma ya umurci jami'an tsaro da su tura sojoji zuwa kan iyakar Kolombiya, yana yiwuwar gargaɗin karuwar 'yan gudun hijira.

Sukukan cikin gida a Amurka

A cikin Amurka, wasu 'yanmajalisar Democrat sun soki harin a matsayin wanda aka kai ba bisa ka'ida ba kuma ba tare da izini ba.

Sanata Ruben Gallego ya ce matakin ya zama "yaki na ba gaira ba dalili na biyu da na gani a rayuwata," yana zargin Washington da shiga cikin rikici haka kawai. "Babu wata hujja da ta sa mu yi yaƙi da Venezuela," in ji shi.

Dan majalisa Jim McGovern ya nuna damuwa game da rashin samun amincewar majalisa da goyon bayan jama'a, yana tambayar dalilin kashe kuɗi a kan ayyukan soja a kasashen waje maimakon abubuwan da suka fi muhimmanci a cikin gida.

‘Yan majalisa sun yi kira ga gwamnatin Burtaniya da ta yi Allah-wadai da Amurka

A Burtaniya, wasu 'yan majalisa sun yi kira ga gwamnati ta yi Allah-wadai da abin da suka bayyana a matsayin hari da ya saɓa doka kan ƙasa mai 'yanci.

‘Yarmajalisa ta indifenda Mewaka Zarah Sultana ta ce dimbin rijiyoyin mai na Venezuela su ne ainihin dalilin harin, tana kiran harin "mulkin mallakar Amurka a fili" da nufin kifar da gwamnati da "kwace albarkatunta." Ta yi kira ga gwamnatin Labour ta Firaminista Keir Starmer da ta yi Allah-wadai da matakin ba tare da wata-wata ba.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Rasha ta yi Allah-wadai da harin a matsayin "hari da makamai", tana cewa hujjojin da Washington ta bayar "ba su da tushe."

Ma'aikatar ta yi gargaɗi kan ƙarin tashin hankali kuma ta ce Moscow a shirye take ta tallafa wajen nemo mafita "ta hanyar tattaunawa", tana jaddada bukatar samun tabbas da bin ƙa'idodin kasa da kasa.

Tarayyar Turai ta yi kira a yi taka tsanstan

Tarayyar Turai ma ta yi kira da a yi taka tsantsan. Babbar Jami’ar harkokin waje ta Tarayya Turai (EU) Kaja Kallas ta ce ta yi magana da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio kuma ƙungiyar na bibiyar lamuran cikin kulawa.

Yayin da ta ƙara jaddada matsayin EU cewa Maduro "ba shi da halcin zama shugaba" ta kuma goyi bayan sauyi cikin lumana a Venezuela, Kallas ta jaddada cewa "a kowane hali, dole a girmama ƙa'idodin dokar kasa da kasa da Yarjejeniya Kafa Majalisar Dinkin Duniya."

Ana ci gaba da kiran a yayyafa wa wutar ruwa yayin da ake ƙara nuna damuwa da tsaron fararen hula, da yaduwar rikici zuwa ƙasashen yankin, da tasirin katsalandan ɗin Sojojin Amurka na dogon lokaci.

Masu AlakaTRT Afrika - An fitar da Shugaba Maduro da matarsa daga Venezuela, in ji Trump
Rumbun Labarai
Tarayyar Afirka ta nuna 'damuwa', Afirka ta Kudu ta nemi a yi taron MDD da gaggawa kan Venezuela
Trump ya gargaɗi Colombia, ya nufi Cuba bayan ya kama Maduro
Amurka ba za ta bari kowa ya ci gaba daga inda Maduro ya tsaya ba - Trump
An fitar da Shugaba Maduro da matarsa daga Venezuela, in ji Trump
Ƙarar bamabamai ta rikita birnin Caracas bayan Trump ya sha alwashin kai hari a ƙasar Venezuela
Zanga-zangar Iran kan matsin tattalin arziki ta rikiɗe zuwa tashin hankali
Hotuna: Wasan tartsatsin wuta da sauran bukukuwa na maraba da Sabuwar Shekara ta 2026
Fiye da mutum 3,000 ne suka mutu a tafiya ci-rani Turai ta Spain a 2025: Rahoto
Somalia ta yi watsi da amincewar da Isra'ila ta yi wa Somaliland a matsayin barazana ga yankin
Turkiyya ta yi tir da Israila kan amincewa da Somaliland
Kiristoci Falasɗinawa sun gudanar da bukukuwan Kirsimeti a Gaza da Gaɓar Yamma
Rasha na shirin gina tashar nukiliya a duniyar wata nan da shekaru 10 masu zuwa
Babban hafsan sojin Libya da jami'ai sun mutu a hatsarin jirgin sama a kusa da Ankara: Dbeibah
Trump ya saka ƙasashen Afirka biyar cikin jerin da ya haramta wa shiga Amurka
Garin da yake shafe kwana 66 a cikin dare babu hasken rana
An kashe sojojin Bangladesh da ke aikin wanzar da zaman lafiya a sansanin MDD na Sudan: Bangladesh
China ta zartar da hukuncin kisa kan tsohon ma'aikacin banki kan karɓar cin hancin dala miliyan 156
Venezuela ta rantsar sabbin sojoji 5,600 yayin da rikici tsakaninta da Amurka ke ƙara tsami
Kundin Guinness World ya dakatar da karbar duk wata buƙata daga Isra’ila: Rahoto
Hotuna: Dubban mutane sun yi maci a Turai da Amurka don nuna wa Falasdinawa goyon baya