FIFA ta ce Afirka ta Kudu ta yi asarar wasan da ta buga da Lesotho na neman buga gasar Kofin Duniya na 2026.
Sanarwar ta FIFA ta ranar Litinin 29 ga Satumba ta ce, an yanke hukuncin ne saboda Afirka ta Kudu ta yi amfani da ɗan wasan da bai cancanta ba.
Afirka ta Kudu ta ci wasan ne da ci 2-0 ranar 21 ga Maris a garin Polokwane, wanda a yanzu aka mayar da shi rashin nasara da ci 3-0.
Hakan na nufin ta koma mataki na biyu a rukunin C, ƙasa da Benin, saboda bambancin ƙwallaye.
A yanzu Lesotho za ta ci gaba da zama a mataki na biyar da maki tara a wasannin na ƙasashen Afrika masu neman cancantar buga kofin duniya mai zuwa.
FIFA ta ce Afirka ta Kudu ta saɓa dokar FIFA saɗara ta 19 ta Ɗa'a, sakamakon amfani da Teboho Mokoena, duk da cewa ɗan wasan ya samu yalon kati biyu a wasanninsu da Benin da kuma Zimbabwe.
Haka nan kuma, Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka ta Kudu za ta biya tarar dala $12,536, duk da cewa za ta iya ɗaukaka ƙara kan hukuncin.
Ƙarin fata ga Nijeriya
Wannan hukunci na FIFA zai bai wa Nijeriya ƙwarin gwiwa saboda a yanzu tana da tazarar maki uku ne kacal a ƙasan Afrika ta Kudu, yayin da ya rage wasanni biyu kafin kammala zagayen a wata mai kamata.
Bayan kammala wasannin, ƙasashe tara ne da suka yi nasara a rukunoni tara ne za su samu cancantar buga gasar Kofin Duniya kai-tsaye.
Daga bisani, ƙasashe huɗu da suka fi yawan maki a bayan tarar, za su buga zagayen share fage, wanda zai iya bai wa Nijeriya matsayin ƙasa ta 10 da za ta samu cancantar buga gasar da za a yi a Amurka, da Canada, da Mexico.