WASANNI
1 minti karatu
Rashford ya sha alwashin kawo wa Barcelona kwallo 40 a bana
Marcus Rashford ɗan wasan Manchester United da ke zaman aro a Barcelona ya sha alwashin ci da ba da tallafin ƙwallo 30 zuwa 40 a kakarsa ta farko.
Rashford ya sha alwashin kawo wa Barcelona kwallo 40 a bana
Shekarun Rashford 27 kuma alamu na nuna yana fatan ci gaba da taka leda a Barcelona / AP
2 Oktoba 2025

Yayin da ya fara kakarsa ta farko a Barcelona cikin sa’a, Marcus Rashford ya sanya wa kansa gagarumin burin cin ƙwallaye a sabuwar ƙungiyarsa ta Barcelona.

Rashford, wanda ke da kwantiragi da Manchester United, ya zo Barca ne a kakar bana a matsayin aro, inda ya fara samun sa’a ƙarƙashin koci Hansi Flick.

A yanzu ɗan wasan mai shekaru 27 ɗan asalin Ingila yana so a ce zuwa ƙarshen kakar bana, ya ci ko ya ba da tallafin cin jimillar ƙwallo 30 zuwa 40.

A halin yanzu bayan buga wa Barca wasanni 9 na La Liga da na Zakarun Turai, ya ci ƙwallo 2 kuma ya tallafa wajen cin ƙwallaye 4.

A wasansu na farko na gasar Zakarun Turai a bana, Marcus Rashford ne ya ciyo wa Barcelona duka ƙwallaye biyun da ta ba su nasara kan Newcastle da ci 2-1.