WASANNI
2 minti karatu
Ronaldo ne ɗan wasan ƙwallo na farko a duniya da ya zama biloniya
Cristiano Ronaldo ya zama ɗan ƙwallon ƙafa na farko da ya mallaki dala biliyan ɗaya, bayan da aka bayyana zunzurutun kuɗin da yake samu daga sabuwar kwantiraginsa da Al-Nassr ta Saudiyya.
Ronaldo ne ɗan wasan ƙwallo na farko a duniya da ya zama biloniya
Cikin 'yan ƙwallon ƙafa, Cristiano ne na farko da ya zama biloniya. / Reuters
8 Oktoba 2025

Tauraron ɗan wasan ƙwallo ɗan asalin Portugal, Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihin zama biloniya na farko a fagen ƙwallon ƙafa a duniya.

Wannan cigaban ya zo wa ɗan wasan mai shekaru 40, sakamakon sabuwar kwantiragin da ya samu daga ƙungiyarsa ta Al-Nassr a Saudiyya a watan Yuni.

Sabon rahoton mujallar Bloomberg ta Amurka ya bayyana cewa Ronaldo na da arziƙin dala biliyan 1.4, saboda kwantiragin shekaru biyu da ya tsawaita da Al-Nassr.

Rahotanni na cewa Ronaldo zai samu albashin dala miliyan 230 duk shekara, wanda ya kai dala 650,000 duk rana, baya ga dala miliyan 32 da ya samu ta rattaba hannu kan kwantiragi.

Da ma dai shiga sahun gwaraza a tarihi ba sabon abu ne ga Cristiano Ronaldo a tsawon rayuwarsa ta ƙwararren ɗan ƙwallo.

Burin da ya rage

Bayan lashe kofuna da dama ga ƙungiyoyin Turai kamar su Manchester United, Real Madrid, da Juventus, Ronaldo ya kasance wanda ya fi buga wa ƙasarsa wasa a tarihi.

Zuwa yanzu, ya zura ƙwallaye 946, fiye da duk wani ɗan wasa a duniya.

Duk da cewa cikin 'yan ƙwallon ƙafa, Cristiano Ronaldo ne na farko da ya zama biloniya, a fannin wasannin motsa-jiki akwai waɗanda suka riga shi cim ma wannan mataki.

Cikinsu akwai Roger Federer ɗan wasan tanis, da Tiger Woods ɗan wasan gora, da Michael Jordan da LeBron James ‘yan wasan ƙwallon kwando.

A halin yanzu dai, babban burin da ya ragewa gwarzon ɗan ƙwallon shi ne cika cin adadin ƙwallaye 1000 kafin ya yi ritaya daga ƙwallon ƙafa, inda yanzu ya rage masa ƙwallaye 54.