Gwamnan jihar Borno a Nijeriya, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi kiran da a faɗaɗa dabarun kawo ƙarshen matsalolin da suka addabi yankin Sahel na Afirka.
Farfesa Zulum ya bayyana wannan ne yayin taron tattaunawar na ASWAN Forum, wanda ake yi a Masar kan Zaman Lafiya Mai Dorewa da Cigaba.
Da yake gabatar da maƙala wajen taron wanda aka yi a birnin Aswan, gwamnan ya nemi ɗaukar matakin kawar da ƙungiyoyin ta’adda da na masu aikata laifuka a yankin Sahel.
Jihar Borno ce inda rikicin Boko Haram ya fi ƙamari tun shekarar 2009, duk da cewa rikicin ya shafi yankin Tafkin Chadi, da ƙasashen Nijeriya, Kamaru, Nijar, da Chadi.
Ya nemi yin aiki tare tsakanin ƙasashen yankin Sahel, wanda ya haɗa ƙasashe 10 a cewa Majalisar inkin Duniya, domin ninka dabarun magance matsalolin tsaro.
Baya ga matsalar tsaro, ya kuma yi nuni da matsalar jinƙai a yankin, yana mai cewa amfani da ƙarfin soji shi kaɗai wajen shawo kan lamura bai wadatar ba.
Ya jaddada cewa akwai buƙatar haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen kawar da tushen rikice-rikice a yankin da ke Yammaci zuwa Tsakiyar Afirka.