Me ya sa hanyoyin teku da aka toshe ke tayar da kura a Gabashin Afirka?
KASUWANCI
6 minti karatu
Me ya sa hanyoyin teku da aka toshe ke tayar da kura a Gabashin Afirka?Kasashen Ethiopia da Uganda da ba su da iyaka da teku na kara kaimi don tabbatar da sun samu damar amfani da tashar jiragen ruwa a yayin da matsin lambar cinikayya ke kara yawa tare da kuma shaida gajen hakurin diflomasiyya.
Tashar jiragen ruwa ta Mombasa a Kenya babbar hanyar teku ce ga kasashen Gabashin Afirka da ba su da iyaka da teku. / Reuters
18 awanni baya

Kasashen da ba su da iyaka da teku a Gabashin Afirka na fafutukar samun isa ga tashoshin jiragen ruwa, yayin da bangarorin da ke da ruwa da tsaki ke da damuwa kan ka’idojin ketare iyakokin kasashe da tsadar kudin sufuri.

Shugaba Yoweri Museveni na Uganda ya yi iyakacin ƙoƙarinsa na yin gargaɗi ga maƙwabciyarsu Kenya kafin daga baya ya rage zafin jawabinsa a watan da ya gabata. Ko da yake na ɗan lokaci ne, amma rashin tabbas ya nuna rashin jin daɗin da aka daɗe ana yi game da damar shiga Tekun India ga Uganda.

"Tekuna ita ce Tekun India," ya bayyana a wani taron manema labarai, yana kwatanta yanayin da wani rukunin gidaje inda mazauna a bene na sama ke da 'yancin shuga lambun da ke wajen daidai da waɗanda ke zaune a ƙasa.

A arewa, ci gaban da Habasha na habaka, wanda ya haɗa da madatsar ruwa mafi girma a Afirka da kuma babban aikin filin jirgin sama a nahiyar, da alama suna samun cikas saboda rashin damar isa ga teku.

Babban ƙofar shigo da kaya ita ce tashar jiragen ruwa ta Tekun Maliya a maƙwabciyarta Djibouti, wadda ke karɓar miliyoyin daloli a kowace shekara a cikin kuɗin amfani da tashar jiragen ruwan, a cewar jami'ai.

Kamfanonin Ethiopia suna kashe ƙarin dala biliyan 1 a kowace shekara a kuɗin sufuri na cikin gida.

Da yawan jama'a da ya haura miliyan 100, Ethiopia ce ƙasar da ta fi yawan jama'a a duniya da ba ta da iyaka da teku. Firaminista Abiy Ahmed ya bayyana ƙudurinsa na sake samun damar shiga Tekun Bahar Maliya, wanda wadda Ethiopia ta rasa lokacin da Eritrea ta balle a 1993. Gwamnatinsa ta dage cewa tana son samun damar shiga teku cikin lumana.

Masana sun ɗora alhakin karuwar rashin jin daɗin shiga tashar jiragen ruwa kan gazawar diflomasiyya da ƙuntatawa da ƙungiyoyin yanki ke fuskanta waɗanda aka kafa don kula da haɗakar tattalin arziki. Sun yi nuni ga gibin da ke tsakanin ƙa'idodin da aka bayyana a cikin yarjejeniyoyin yanki da hanyoyin gudanarwa da ma'aikatan gwamnati ke aiwatarwa.

"Abin da ke kan takarda kuma a aikace abubuwa biyu ne daban-daban. Idan ana maganar aiwatarwa, ko dai aiwatar da wani bangare ko kuma biyan buƙatun mutum ɗaya ne ke zuwa. Wannan batu ne da ke shafar ƙasashe da yawa da ba su da iyaka da teku a yankin," in ji Farfesa David Mugisha, wani masanin harkokin ƙasashen duniya na Uganda, yayin tattaunawa da TRT Afrika.

Muhimman bukatu mabambanta

Duk da cewa damuwar Habasha ta ta'allaka ne kan hauhawar farashin cinikayya da kuma samun damar shiga kasuwannin duniya, Uganda ta zabi dogaro kan siyasa da manufofin makwabtanta a matsayin raunin da ya zama dole ta kawar da shi daga wannan lissafi.

Uganda na haduwa da Tekun India ta hanyoyin sufuri da ke ratsa Kenya da Tanzania, suna haduwa da tashoshin jiragen ruwa na Mombasa da Dar es Salaam a jejjere.

An gabatar da wani bututun mai da ke tashi daga rijiyoyin mai a arewa da yammacin Uganda zuwa tashar jiragen ruwa ta Lamu ta Kenya a shekarar 2016 bayan da Shugaba Museveni ya zabi hanyar da ta fi gajarta kasa da ta Tanzania zuwa tashar jiragen ruwa ta Tanga.

A halin yanzu, yawan mai da aka tabbatar da gano wa a kasar ya kai kusan ganga biliyan 6.6, tare da ganga biliyan 1.6 da za a iya hakowa bisa ga bayanai daga ma'aikatar makamashi.

Ana sa ran fara hako man a shekara mai zuwa, wanda ya bayyana dalilin da ya sa muryar Kampala ya kara yin tsauri kan al'amuran yankin wanda za su iya yin tasiri ga wannan bangare.

Shugaba Museveni ya yi magana a watan da ya gabata game da buƙatar haɗin gwiwa tsakanin maƙwabtan uku don kare gabar tekun, wanda ya jaddada cewa kadara ce ta bai daya maimakon mallakar ƙasa daya kawai.

"Akwai batun dabarun tsaro. Duk da muna tare a cikin Ƙungiyar Gabashin Afirka (EAC), ba ma tsara manufofin tsaro tare. Shi ya sa na ke magana game da haɗin gwiwar siyasa; ra'ayin shi ne mu ƙara ƙarfinmu," in ji shi.

A matsayinmu na wanda ya shafe kusan shekaru 40 yana kan mulki, Museveni ya fuskanci bambance-bambancen ra'ayoyi na shugabannin Tanzania biyar da huɗu na Kenya tare da rashin zaman lafiya da ya biyo bayan zaɓen Kenya a 2007 da kuma zaɓen da aka gudanar kwanan nan a Tanzania.

Masu sharhi na yin jayayya cewa Shugaban Uganda na neman tabbacin samun damar shiga Tekun India don kare ƙasar daga sauye-sauyen shugabanci a ƙasashen da ke makwabtaka.

"Ina ganin diflomasiyya ta taka rawar gani, kuma an cim ma abubuwa da yawa, amma saurin tafiyar da abubuwa ke yi, da kuma ganin cewa Museveni ya shafe shekaru 40 yana mulki, ina ganin akwai abubuwa da yawa da mutum zai iya ɗauka. Don haka, ba wai yana magana ne kawai don tayar da hankali ba, a’a yana fuskanci kalubale da cikas da dama na takaici," in ji Farfesa Mugisha.

Tashar kiranye ta Ethiopia

Ethiopia na a wajen da ke da nisan ƙasa da kilomita 80 daga Tekun Maliya amma wani yanki na ƙasar Eritrea ya toshe ta.

Asmara ta zargi maƙwabciyarta da ba ta da iyaka da teku da shirin kwace tashar jiragen ruwanta da ke Assab, duk da cewa Firaministan Ethiopia Abiy Ahmed ya musanta shirin duk wani mataki na kai hari don samun damar shiga tekun. Ahmed ya bayyana batun shiga Tekun Maliya a matsayin "matsalar rayuwa".

Ƙasashen biyu sun sami daidaito da ya kafa tarihi, wanda saboda ita Abiy ya lashe kambin Nobel Peace Prize a 2019. Amma tun daga lokacin sun raba gari.

Yunkurin Ethiopia a watan Janairun 2024 na hayar wani yanki mai tsawon kilomita 20 na bakin teku a yankin Somaliland da ya balle daga Somalia ya haifar da rikicin diflomasiyya, inda Mogadishu ta zargi Ethiopia da cin dunduniyar ‘yancin kasarta a yankin.

Ƙoƙarin shiga tsakani na Turkiyya ya shimfida harsashin sulhu tsakanin maƙwabtan biyu, wanda ya kai ga sanarwar Ankara mai tarihi inda Firaminista Abiy da Shugaba Hassan Sheikh Mohamud na Somalia suka amince su girmama ikon kowanne bangare.

Duk da haka, Abiy ya ci gaba da bayyana burinsa na gina tashar jiragen ruwa. Ya shaida wa 'yan majalisar dokokin Ethiopia a watan Oktoba cewa yana da "tabbacin cewa miliyan bisa miliyan" Ethiopia ba za ta ci gaba da zama cikin mawuyacin hali ba, "ko da wani ya so ko bai so ba".