NIJERIYA
3 minti karatu
EFCC ta ƙwato naira biliyan 500 tare da samun mutum 7,000 da laifi cikin shekara biyu — Tinubu
Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa gwamnatinsa ba ta saka baki a ayyukan hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa ko ɓangaren shari’a ba, yana mai cewa an bai wa dukkansu biyu damar ayyukansu yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
EFCC ta ƙwato naira biliyan 500 tare da samun mutum 7,000 da laifi cikin shekara biyu — Tinubu
Bola Tinubu ya ƙara da cewa kadarorin da aka ƙwacen ana amfani da su a shirin bai wa ɗalibai bashin kuɗin makaranta / Reuters
17 awanni baya

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce hukumar EFCC, mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasar zagon ƙasa ta yi nasarar samun mutum 7,000 da laifi tare da ƙwato kadarori da ƙimarsu ta kai naira biliyan 500 cikin shekaru biyu a ƙarƙashin mulkinsa.

Da yake magana ranar Litinin a wani taron bita da EFCC ta shirya wa alƙalai a makarantar horas da ma’aikatan shari’a na Nijeriya da ke Abuja, shugaban  wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Kashim Shettima, ya ce alƙaluma sun nuna jajircewar gwamnatinsa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma ‘yanci a ɓangaren shari’a.

“Hukumar EFCC ta yi nasarar samun sama da mutum dubu bakwai da laifi a cikin shekara biyu na farko na gwamnatina tare da ƙwato kadarori da ƙimarsu ta zarce naira biliyan ɗari biyar,” a cewar Tinubu.

Ya ƙara da cewa kadarorin da aka ƙwacen ana amfani da su ne kan shirye-shiryen zamantakewa ciki har da shirin bai wa ɗalibai aron kuɗin makaranta da kuma shirin bai wa mutane bashin kuɗaɗe.

Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa gwamnatinsa ba ta saka baki a ayyukan hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa ko ɓangaren shari’a ba, yana mai cewa an bai wa dukkansu biyu damar ayyukansu yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

“Babu wani mutum ko kuma wasu mutane da za su iya zargin wannan gwamnatin cewa tana kare ‘yan siyasa domin alaƙarsu da wannan gwamnatin ko kuma jam’iyyar siyasarmu,” in ji shi.

“Mun bai wa ɓangaren shari’a da kuma hukumomi masu yaƙi da cin hanci da rashawa ‘yanci domin su yi ayyukansu yadda kundin tsarin mulki ya tanada.”

Da yake jawabi ga jami’an ɓangaren shari’a a bitar wadda wannan ne karo na bakwai da ake shirya ta, Tinubu ya amince cewa akwai takaici game da jinkirin da ake samu wajen shari’a kan cin hanci da rashawa yayin da ake gaggauta shari’a kan masu zamba ta intanet.

“Taken bitar ta wannan shekarar, ‘Inganta adalci a yaƙi da laifukan yi wa tattalin arziki zagon ƙasa’, zai ja hankalin mutane da yawa cikin taron nan, inda yake zuwa a wani lokaci da tattaunawa kan yaƙi da cin hanci da rashawa ke janyo ɓacin rai kan jinkiri wajen yanke hukunci kan manyan shari’un cin hanci da rasahawa yayin da ake gaggauta yanke hukunci kan batutuwa da suka shafi zamba ta intanet,” in ji shugaban ƙasar.

“Akwai kuma wani mataki na ɓacin rai game da hukunce-hukuncen da kotu ke yankewa kan mahimman shari’u na cin hanci da rashawa da ke sa mutane suna jin ana cutar al’umma.”

Tinubu ya yi kira da alƙalai su ƙarfafa mutuncin tsarin shari’a, wanda ya bayyana a matsayin “mafaka ta ƙarshe ga duk zukatunmu.”

 “Wata Nijeriya wadda ta barranta daga cin hanci da rashawa za ta iya samuwa idan dukkanmu muka duƙufa ga yin abin da ya dace a duk inda muke da iko,” in ji shi.