WASANNI
2 minti karatu
Ɗan ƙwallon Togo ya karya wuyansa a China bayan ya yi karo da allon talla
Samuel Asamoah ya samu karaya a wuya da kuma lahani a jijiyoyi bayan abokin karawarsa ya ture shi yayin wani wasa a China.
Ɗan ƙwallon Togo ya karya wuyansa a China bayan ya yi karo da allon talla
Togolese Samuel Asamoah hit his head on a billboard, his club said. / Reuters
9 Oktoba 2025

Ɗan wasan ƙwallon ƙafa ɗan ƙasar Togo, Samuel Asamoah, ya karya wuyansa bayan yin karo da allon talla da ke kusa da filin wasa, yayin wata gasa ta gida a China, a cewar kulob dinsa.

Kulob ɗin ya ce suna tsoron cewa zai iya zama nakasasshe sakamakon raunin.

Bidiyon da aka ɗauka ya nuna sanda wani abokin hamayyar ɗan wasan mai shekaru 31, ya ture shi yayin wani wasa da aka buga ranar Lahadi a gasar League One ta mataki na biyu a ƙasar.

Yayin da suke turereniya don karɓe ƙwallo, an ture Asamoah kuma ya yi karo da kai da wani allon talla na LED.

Kulob ɗin nasa, Guangxi Pingguo, ya bayyana cewa Asamoah ya samu karaya a wuya da kuma lahani a jijiyoyi, sannan an yi masa tiyata.

"Yana cikin mummunan haɗarin samun nakasa mai tsanani, kuma ba zai iya buga sauran wasannin kakar nan ba. Haka kuma, rayuwar wasansa na iya fuskantar babban tasiri," in ji kulob ɗin a ranar Litinin.

Farfaɗowa daga tiyata

Ranar Laraba kulob ɗinsa ya ce Asamoah yana murmurewa daga tiyatar da aka yi masa, kuma yanayinsa ya fara daidaita.

Ƙungiyar ta ce, "Guangxi Pingguo FC tana matuƙar godiya ga masoya a ko ina saboda nuna damuwa da goyon baya ga Samuel Asamoah".

"Za mu sanar da sabbin bayanai game da warakarsa kan lokaci, bayan an ci gaba da duba lafiyarsa."

Asamoah ya kwashe yawancin shekarun wasansa a Belgium, kafin ya koma China a bara.

Buga wa Togo

Samuel Asamoah ya buga wa ƙasarsa Togo wasa sau shida, cewar shafin tattara bayanan wasannin ƙwallon ƙafa na transfermarkt.com.

Wata kafar labarai ta yankin da ta ambato hukumomin ƙwallo a China ta ce, an kafa allon tallan tazarar mita uku daga filin wasan, daidai da dokokin duniya.

A yayin wasan, an bai wa Zhang Zhixiong, ɗan wasan ƙungiyar Chongqing Tonglianglong, wanda ya tur Asamoah yalon kati, bayan abin da ya faru.