Shugaban Amurka Donald Trump ranar Asabar ya yi gargaɗi mai ƙarfi ga shugaban Colombia Gustavo Petro bayan wasu munanan hare-hare da Amurka ta kai Venezuela sannan ta kama shugaban ƙasar Nicolas Maduro tare da fitar da shi daga ƙasar.
Kazalika ya ja kunnen shugaban Cuba.
Yayin da yake mayar da martani game da tsokacin Petro ya yi kan tasirin da hare-haren Venezuela za su iya yi, Trump ya shaida wa wani taron manema labarai a Florida cewa shugaban na Colombia yana kan gaba wajen samar da miyagun ƙwayoyi tare da yin safararsu zuwa cikin Amurka.

“Yana da kamfanonin samar da odar koken. Kuma suna tura ta zuwa Amurka. Don haka Petro ya kiyayi kansa,” in ji Trump.”
Gabanin kai hare-hare Venezuela tare da kama shugabana ƙasar, Trump ya sha nanata zargin da yake yi wa Caracas na shigar da miyagun ƙwayoyi cikin Amurka, inda ya ce an kai hare-haren ne domin magance wannan bala’i da ya addabi yankinsu.
Nan ba da jimawa ba Amurka za ta waiwayi Cuba
Trump ya caccaki Cuba, inda ya bayyana ƙasar a matsayin “ƙasar da ta gaza” sannan ya ɗora alhakin matsin tattalin arzikin da ta kwashe shekaru tana fama da shi kan shugabanninta. Ya ce nan ba da jimawa ba Amurka za ta waiwayi Cuba.
“Al’ummar ƙasar sun kwashe shekaru aru-aru suna cikin wahala. Muna so mu taimaka wa al’ummar ƙasar Cuba, kuma muna so mu taimaka wa mutanen da aka kora daga Cuba ƙarfi-da-yaji da waɗanda suke zaune a ƙasar,” in ji Trump.












