Sakataren Wajen Amurka Marco Rubio ya yi kira ga masu ruwa da tsaki na ƙasashen duniya su daina bayar da makamai ga mayaƙan rundunar Rapid Support Forces na Sudan, inda ya ɗora musu alhakin ta’azzarar zubar da jini a ƙasar.
"Ina gani ya kamata a yi wani abu domin daina bayar da makamai da goyon baya ga RSF a yayin da suke ci gaba da ƙaimi da mamaye wurare," a cewar Rubio a hira da manema labarai ranar Laraba a yayin da yake barin wurin taron ministocin ƙasashen waje na ƙungiyar ƙasashen (G7) a Canada.
Ministocin ƙasashen waje na ƙungiyar G7 sun yi Allah wadai bisa “hare-haren ƙalibanci” da mayaƙan Rapid Support Forces (RSF) da ke Sudan suke kai wa fararen-hula da ba su da laifi da kuma ma’aikatan agaji a Al Fasher da North Kordofan.

Wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar bayan kammala taron na kwanaki biyu a Niagara, Canada, manyan jami’an diflomasiyya daga ƙasashen Canada, Faransa, Jamus, Italiya, Japan, Birtaniya da Amurka — tare da wakilin Hukumar Tarayyar Turai — sun yi kakkausar suka game da "mummunan tasirin da wannan yaƙi yake yi a kan fararen-hula, ciki har da matsananciyar yunwa da ta haddasa larurar rashin jinkai mafi muni a duniya."
"Mun yi Allah wadai da da kakkausar murya kan yadda ake yin lalata da mata. Muna kira ga dakarun Rapid Support Forces (RSF) da na Rundunar Sojin Sudan (SAF) su yi biyayya ga tsarin kare hakkin ɗan’adam, tare da tsagaita wuta nan-take da kuma bari a shigar da kayan agaji ba tare da jinkiri ba," in ji sanarwar da suka fitar ranar Laraba.
Kazalika ministocin sun nuna goyon bayansu ga “yunƙurin diflomasiyya da ake yi na maido da zaman lafiya da tsaro” tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki na ƙasashen duniya su bayar da tasu gudunmawar wajen tabbatar da zaman lafiya.
An kashe dubban mutane, an raba miliyoyi da matsugunansu
Hakan na faruwa ne a yayin da MDD ta yi gargaɗi cewa halin da ake ciki a Sudan yana ci gaba da taɓarɓarewa musamman ga fararen-hula, sannan ƙungiyoyin bayar da agaji sun ce suna fuskantar kalubale wajen shiga yankunan da yaƙin ya shafa.
An soma yaƙi tsakanin sojojin Sudan da mayaƙan RSF a watan Afrilun 2023, kuma kawo yanzu ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 40,000 tare da raba fiye da mutum miliyan 12 da muhallansu, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.



















