Shugaba Donald Trump ya sanya hannu kan wata takardar da ke nuna cewa za a janye Amurka daga ƙungiyoyi da dama na ƙasa da ƙasa, ciki har da hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya, in ji Fadar White House.
"A yau, Shugaba Donald J. Trump ya sanya hannu kan wata takardar da ke nuna cewa za a janye Amurka daga ƙungiyoyi 66 na ƙasa da ƙasa waɗanda ba sa ci gaba da biyan buƙatun Amurka, ciki har da: ƙungiyoyi 35 waɗanda ba na Majalisar Ɗinkin Duniya ba da kuma ƙungiyoyi 31 na Majalisar Ɗinkin Duniya," in ji Fadar White House a ranar Laraba.
Fadar White House ba ta lissafo ƙungiyoyin ba amma ta ce suna yaɗa "manufofin sauyin yanayi masu tsauri, shugabancin duniya, da aƙidu waɗanda suka saɓa wa iko da tattalin arzikin Amurka."

Ta ce matakin ya samo asali ne sakamakon bita da aka yi kan dukkan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, manyan tarukan ƙulla ƙawance da yarjejeniyoyin da Amurka ke ciki ko kuma take mamba.
"Wannan janyewar za ta kawo ƙarshen bayar da tallafi da kuɗaɗen masu biyan haraji na Amurka da kuma shiga cikin ƙungiyoyin da ke haɓaka manufofin duniya fiye da fifita buƙatun Amurka, ko kuma waɗanda ke magance muhimman batutuwa ba tare da inganci ko alfanu ba, ta yadda a yanzu za a ware kuɗaɗen masu bayar da haraji na Amurka ga wasu hanyoyi don tallafa wa ayyukan da suka dace," in ji Fadar White House.
Tun lokacin da ya fara wa'adinsa na biyu shekara guda da ta gabata, Trump ya nemi rage kudaden da Amurka ke bai wa Majalisar Ɗinkin Duniya, ya dakatar da hulɗar Amurka da Hukumar Kare Hakkin Ɗan’adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ya tsawaita dakatar da tallafin da ake bai wa hukumar agaji ta Falasɗinu UNRWA da kuma ficecwa daga Hukumar Raya Al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO. Ya kuma sanar da shirin fice wa daga Hukumar Lafiya ta Duniya da yarjejeniyar yanayi ta Paris.











