Jami’an hukumar shige da fice da hana fasa-ƙauri ta Amurka (ICE) sun tsare Ken Ofori-Atta, tsohon Ministan Kuɗin Ghana.
A cewar lauyoyinsa, Minkah-Premo, Osei-Bonsu, Bruce-Cathline and Partners (MPOBB) kamun da aka yi wa Ofori-Atta na da alaƙa da yanayin zaman da yake yi a Amurka a yanzu.
A cikin wata sanarwa da suka fitar ranar Laraba da daddare, sun bayyana cewa tawagar lauyoyinsa a Amurka na tuntuɓar hukumar ICE kuma suna tsammanin za a warware matsalar cikin sauri.
"Mista Ofori-Atta yana da takardar neman gyara matsayin zamansa, wanda ke bai wa mutum izinin zama a Amurka bisa doka bayan lokacin da takardar izinin zama a ƙasar ta daina aiki. A ƙarƙashin dokar Amurka, canjin matsayi ta wannan hanyar abu ne da aka saba yi," in ji sanarwar.
"Saboda haka, ana kira ga jama'a da su lura cewa shi mutum ne mai bin doka kuma yana ba da cikakken haɗin kai ga ICE don a warware wannan matsalar", in ji sanarwar.

Tsohon Ministan Kuɗi, Kenneth Ofori-Atta da wasu mutane bakwai na fuskantar tuhume-tuhume 78 kan kwangilolin da aka bai wa Strategic Mobilisation Ghana Limited (SML).
A bisa tuhumar da Ofishin Mai Gabatar da Ƙara na Musamman (OSP) ya shigar a watan Nuwamban 2025, ana zargin mutanen da almundahanar kuɗaɗen sayo kayayyakin da aka bai wa kamfanin SML kwangilar kaiwa Ghana. Sun yi ƙoƙarin amfani da Ma’aikatar Kuɗi ta Ghana da Hukumar Tattara Haraji ta Ghana.
A cewar OSP, wannan kamfanin aikata laifuka ya fara aiki ne a shekarar 2017.
Ken Ofori-Atta ya kasance a Amurka tun daga watan Janairun 2025 saboda dalilai na neman lafiya.
Ofishin Mai Gabatar da Ƙara na Musamman ya sanya shi a cikin sanarwar ‘yansandan ƙasa da ƙasa a matsayin mutumin da ake nema ruwa-a-jallo saboda amfani da ofishin gwamnati don amfanar da kai, matakin da yake ƙalubalanta.















