Aƙalla mutum 570 sun tsere daga matsugunansu a birnin Kadugli da ke Kudancin Kordofan a cikin kwana uku sakamakon tabarɓarewar yaƙi, a cewar wata sanarwa da Hukumar Kula da Masu Ƙaura ta Duniya (IOM) ta fitar ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce tawagogin hukumar da ke bibiyar lamura a yankin sun shaida mata cewa mutum 570 sun tsere daga gidajensu a Kadugli daga ranar 8 zuwa 10 ga watan Janairu, a yayin da hare-hare suka yi ƙamari a birnin.
Mutanen sun nufi Jihar White Nile da ke Kudancin Sudan.
Halin da ake ciki a Kadugli yana cike da “rashin tabbas da hatsari,” a cewar OIM, inda ta ƙara da cewa tawagoginta suna ci gaba da sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a yankin.
A makon jiya, IOM ta ce adadin mutanen da suka fice daga gidajensu a jihohi uku na Kordofan, Arewaci, Yammaci da Kudanci, ya ƙaru zuwa 64,890 daga ranar 25 zuwa 30 ga Oktoban 2025.
Rikici ya yi ƙamari a makonnin baya bayan nan a faɗin jihohi uku na Kordofan, inda sojojin Sudan da mayaƙan Rapid Support Forces (RSF) suka tilasta wa dubban fararen-hula tserewa daga matsugunansu.
A cikin jihohi 18 na Sudan, mayaƙan RSF na riƙe da ikon dukka jihohi biyar da ke yankin Darfur a yammacin ƙasar, ban da wasu tsirarun jihohi da ke Arewacin Darfur wadanda ke ƙarƙashin ikon sojojin gwamnati.
A gefe ɗaya, rundunar sojin ƙasar na riƙe da jihohi 13 da ke kudanci, arewaci, gabashi da da kuma yankin tsakiyar Sudan, ciki har da Khartoum, babban birnin ƙasar.
Yaƙin Sudan, wanda ya ɓarke tsakanin sojoji da dakarun RSF tun watan Afrilun 2023, ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu.








