Nijeriya na sa ran ganin sakamako mai kyau bayan aiwatar da wani kyakkyawan tsari a harkar kamfanoni
KASUWANCI
4 minti karatu
Nijeriya na sa ran ganin sakamako mai kyau bayan aiwatar da wani kyakkyawan tsari a harkar kamfanoniRibar da kamfanoni ke samu a Nijeriya ta habaka sosai a yayin da ake yin sauye-sauye, amma kuma ribar da kamfanonin ke samu ta sha bamban da juna, inda karfin aljihun iyalai ke ragu wa.
Nijeriya na daya daga manyan kasashen Afirka mafiya karfin tattalin arziki inda gwamnati ke ta kokarin kmawo sauye-sauye.
4 Agusta 2025

Alkaluman da ke fito wa daga kamfanonin Nijeriya na zama masu ban mamaki.

Kamfanoni da dama sun bayyana samun karin riba da kashi 500. Hannayen jarinsu sun ninka, a wasu wuraren ma ribar da aka samu ta ninninka.

Masu zuba jari da suka sayi hannayen jarin bankuna shekaru biyu da suka gabata, a yanzu na bibiyar Naira 44 (dala 0.029) da suka zuba jari a matsayin sama da Naira 100 (dala 0.065).

Amma ga kowace irin nasara a yankunan kasuwanci na Legas, akwai kuma wahalhalu da ake sha a kan titunan Nijeriya.

Irin wadannan manufofin habaka tattalin arziki da suka samar da garabasa ga kamfanoni dai- za a iya cewa janye tallafin man fetur da karyewar darajar kudi - sun rage karfin sayen kayayyaki na ‘yan Nijeriya.

Yawan ribar da kamfanonin Nijeriya suka bayyana sun samu na da ban ta’ajibi, wanda ya kalubalanci lokacin da ya gabaci na yanzu.

Karyewar darajar kudin kasar ya taimaka wajen raguwar riba a shekarar da ta gabata,” in ji Kasim Garba Kurfi, Shugaban kamfanin ‘APT Securities and Funds’ a tattaunawar sa da TRT Afrika.

Bayan 2024 da aka sha wahalahlau, Babban Bankin Nijeriya ya yi kokarin daidaita farashin kudin kasashen waje a wannan shekarar, inda ya tsayar da Naira a mataki guda yayin mu’mala da sauran kudaden waje.

“Kamfanonin Nijeriya sun dakatar da bayyana yin asarar kudaden kasashen waje. Sakamakon haka, ribarsu ta karu sama da ninki biyu,” in ji Kurfi.

“Wadanda suka zuba jari a lokacin da aka fada matsala, a yanzu su ne suka fi kowa morewa.”

Rukunin kamfanonin Dangote ya bayyana samun ribar Naira biliyan 418 a watanni uku na biyu, wanda hakan ke nufin kari da kashi 250 a shekara bayan shekara.

Kamfanin Okomu Oil, wanda ke samar da manja, ya haura hasashen da ya yi inda ya bayyana samun ribar biliyan 34.841 a watanni uku-uku. Ribar ta karu da kashi 459.

Rashin daidaiton riba

A wannan gaba ne ake fama da matsala babba a tattalin arzikin Nijeriya.

A yayin da kasa ke dabbaka manufofin cigaban tattalin arziki na zamanin yau, wasu mutanen na kara zama masu arziki yayin da wasu kuma suke kara talauce wa, wanda hakan ke kawo babbar tazara a rabon tattalin arziki.

Tsare-tsaren da suka kubutar da kamfanoni daga asarar kudaden kasashen waje, sun kawo wahalhalu da dama ga ‘yan kasa, baya da radadin janye tallafin mai da karyewar kudade da suke fama da shi.

Babban matakin da gwamnati ta dauka ya mayar da hankali kan sake dora alhakin haraji ta hanyar kawo sabbin dokoki. An cire wani bangare na ‘yan Nijeriya daga biyan haraji kwata-kwata.

A yanzu a Nijeriya an janye haraji ga masi samun kasa da Naira 108,000 a wata da kasa da Naira miliyan 1,300,000 a shekara.

“Mun janye haraji ga mutanen da suke kasa da ba sa samun wasu kudade. Mun rage yawan harajin masu matsakaicin samun kudi, sannan mun dan kara yawan kudin harajin ga masu hannu da shuni,” in ji Taiwo Oyedele, shugaban Kwamitin Shugaban Kasa Sauye-Sauyen Manufofin Kudi da Tattara Haraji a wata tattauna wa da ya yi kwanan nan.

Fatan tallafa wa talaka

A yayin da aka tsara shirin don daidaita lissafin, karbar harajin bai kankama ba.

Kwararru na cewa yadda gwamnati ke kashe kudaden da ta samu daga haraji ne zai tabbatar da ko ribar da kamfanoni ke samu za ta amfani wadanda a yanzu aka bari a baya.

“A duk lokacin da kamfani ya bayyana ribar da ya samu kuma gwamnati ta karbi kashi 30 na ribar da ya samu, to dan kasa gama-gari zai amfani kudin ne idan aka kashe a bangaren jin dadi da walwalar jama’a,” Kurfi ya fada wa TRt Afrika.

Yana son gwamnati ta karkatar da karin kudaden haraji zuwa ga samar da kayan rage radadin wahala ga talakawa da inganta kayan more rayuwa - wutar lantarki, hanyoyi da makamashi - da za su amfani kowa.

Har ma ga wadanda suke da dan abin hannunsu, Kurfi ya bayar da shawarar shiga kasuwanci. “Asali, ya kamata kowa ya zuba jarin dan abinda yake da shi a kasuwannin hannayen jari ta yadda za su dinga amfana da ribar da ake rarraba wa duk bayan watanni,” in ji shi.

Duk da kalubalen, ana kallon nasarar kamfanonin Nijeriya a matsayin wata babbar dama ta kara yawan habakar jama’a.

Kwararru sun yi gargadin cewa ba tare da samun rabon arzikin kasa ga dukkan ‘yan Nijeriya ba, kasar z ata fada hatsarin samar da tattalin arziki biu da ke cin karo da juna, inda masu kudi za su ci gaba da jin dadi, sauran ‘yan kasa gama-gari kuma su ci gaba da kasancewa a cikin talauci.

Rumbun Labarai
Ana hasashen mambobin OPEC+ za su ƙara yawan fetur ɗin da suke fitarwa yayin da farashinsa ke karewa
Gwamnatin ƙasar Ghana ta ƙara farashin koko
Nijar ta samu tallafin $145m daga bankin AfDB domin inganta makamashi da tattalin arziki
Elon Musk na dab da zama mutum na farko da arzikinsa ya kai tiriliyan a duniya: rahoto
Dangote zai mai da ma'aikatan Matatar Mai da aka kora daga aiki - Ma'aikatar Ƙwadagon Nijeriya
Kamfanin Orano na Faransa ya ce ya tara tan 1,500 na uranium a Nijar
Kamfanonin haɗin gwiwa ƙarƙashin Saudiyya za su sayi kamfanin wasannin game na Electronic Arts (EA)
Kamfanin Turkish Airlines zai sayi jiragen sama na Boeing 225 bayan Trump da Erdogan sun tattauna
Hukumomi a Ghana sun kama mutanen da ake zargi da yin fasa-ƙwaurin zinari
Matatar mai ta Dangote ta yi watsi da jita-jitar dakatar da aiki na wasu watanni
Babban Bankin Ghana ya dakatar da lasisin cinikin kuɗin ƙetare na UBA da wasu manhajojin aika kuɗi
Farashin ƙwallon kaɗanya ya faɗi warwas a Nijeriya bayan ƙasar ta dakatar da fitar da shi
Babban Bankin Ghana ya ba da sabbin sharuɗɗan kuɗaɗen ƙetare ga masu shiga da kayayyaki
Madogarar bincike kan abincin da aka sauya wa halitta (GMO), da dalilan karɓuwarsa a Nijeriya
Manoman koko a Ghana sun fi takwarorinsu samun farashi mai kyawu a Yammacin Afirka – COCOBOD
Kamfanin Tsaro na Turkiyya zai ƙulla yarjejeniya da Malaysia don samar mata da motocin yaƙi
Turkiyya da Libya sun kulla yarjejeniyar hakar ma’adanai, samar da makamashi da ababen more rayuwa
Filin jiragen sama na Istanbul ya sake cirar tutar tashin jirage a Turai, in ji Ministan Sufuri
China da Amurka sun cim ma yarjejeniyar kasuwanci
Shugaban Nijeriya Tinubu ya sanya hannu a kan sababbin Dokokin Haraji