Nyashinski Ya kamata a ce Nyashinski ne ya jagoranci Bikin Madaraka. / Hoto: Nyashinski

Shahararren mawaƙin nan na Kenya Nyamari Ongegu wanda aka fi sani da Nyashinski, ya janye daga bikin da za a yi na USA Madaraka 2024 bayan ya gaza samun biza ga 'yan tawagarsa.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Nyashinski, wanda ya samu kyauta ta East Africa Acts Entertainment Awards 2022, ya ce ba zai yi wasa a wurin bikin ba duk da ƙokarin da aka yi na nemar wa 'yan tawagarsa biza a zuwa Amurka.

"Mun yi matuƙar son zuwa wurin wannan bikin, muna bayar da haƙuri kan wannan matsalar da ta faru," kamar yadda Nyashinski ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.

Muna baƙin cikin sanar da cewa sakamakon wasu abubuwa da suka fi ƙarfinmu, ba za mu iya halartar taron ‘USA Madaraka Festival 2024’ ba. Duk da kyakkyawan ƙoƙarin waɗanda suka shirya gasar, amma ba su iya samar wa ‘yan tawagarmu Visa ta shiga Amurka ba. Mun yi niyya da shan alwashin halartar gasar, kuma muna neman gafarar mutane sakamakon wannan abu na rashin jin daɗi.

Bikin Madaraka biki ne na waƙoƙin Afirka da al'adu da al'ummomi waɗanda ake shiryawa a faɗin biranen Amurka.

Bikin na 2024, wanda shi ne irinsa na goma, za a soma gudanar da shi a ranar 25 ga watan Mayu a birnin Dallas inda za a kammala a shi a ranakun 17 da 18 ga watan Yuni a birnin Seattle.

Kamar yadda waɗanda suka shirya taron suka bayyana, Nyashinski yana daga cikin jagororin bikin tare da Eddy Kenzo wanda mawaƙin Uganda ne da Naomi Achu daga ƙasar Kamaru.

Sauran su ne mawaƙin Sudan ta Kudu Dynamq da na ƙasar Ƙenya mai kiɗan ganga Savara.

Ya dawo zuwa Kenya a 2016 don ci gaba da waƙoƙinsa.

Yawaitar hana Biza

Mawaƙa da makaɗan Afirka na yawan fuskantar wahalhalu wajen samun biza domin tafiya ƙasashen Turai, kuma babu wani dalilin hana bayar da bizar.

Wannan yana janyo ƙorafi a shafukn sada zumunta daga mawaƙan.

A watan Janairun 2023, Emma Nzioka, mawaƙiyar Kenya kuma DJ da aka fi sani da Coco Em, ta so zuwa Cape Verde inda za ta bi ta ƙasar Netherlands.

Coco Em ta yi magana kan hana mawaƙan Afirka biza da ake yi. Hoto: Coco Em

Amma an hana Coco bizar ya da zango a ƙasar wanda ya janyo ƙorafi daga magoya bayanta a shafukan sada zumunta.

Wata mawaƙiyar Afirka ma ita ce ƙwararriyar kiɗan Afripop daga Nijeriya, an hana ta bizar Schengen a watan Janairun 2023.

A 2022, an hana Alade biza ta zuwa Canada don halartar bikin Daren Ƙasa da Ƙasa na Afirka.

A 2019, an hana mawakan Tanzania biyu DJ Duke da MCZO biza ta zuwa Amurka.

Magoya bayan sun soki wannan mataki, suna masu kiran su da "yin watsi da mawaƙan Afirka" baki ɗaya.

TRT Afrika