RAYUWA
2 minti karatu
Yadda ɗaliban Nijeriya suka samu zantawa da ‘yar-sama-jannati da ke Tashar ISS a sararin samaniya
Wasu ɗalibai a Nijeriya sun zanta kai-tsaye da wata ‘yar-sama-jannati Zena Cardman, a yayin da take shawagi a sararin samaniya.
Yadda ɗaliban Nijeriya suka samu zantawa da ‘yar-sama-jannati da ke Tashar ISS a sararin samaniya
/ NEWS
5 awanni baya

A wani lamari mai cike da tarihi a fannin binciken sararin samaniya a Nijeriya, ɗalibai daga makarantu 20 a babban birnin tarayyar ƙasar, Abuja sun samu damar zantawa da ‘yan-sama-jannati.

Zantawar an yi ta ne kai-tsaye da Zena Cardman, wata ‘yan-sama-jannati yayin da take shawagi a cikin Tashar Ƙasa-da-Ƙasa da ke Sararin Samaniya, wato ISS.

Hukumar Sararin Samaniya ta Nijeriya (NASRDA), ta haɗa jonin fasahar Amateur Radio don saduwa da tashar ARISS, don bai wa ɗalibai gagarumin abin tunawa.

Shirin ya samu kulawar Stefan Danbooski, wanda ke zaune a Belgium, yayin da John Sygo ya jagoranci tashar da ke duniya a Afirka ta Kudu, daga inda aka haɗa jonin.

Ɗaliban sun yi sauraro cikin natsuwa yayin da suke miƙa tambayoyi kan kimiyya, rayuwa a falaki, da kuma makomar ɗan-adam a samaniya.

Tambayoyin hikima

Cikin tambayoyin da ɗalibai suka yi, akwai “Yaya ku ke barci a yanayin rashin maganadisu?”

Zena ta bayyana cewa ‘yan-sama-jannati suna barci a ɗan ƙaramin kwanson da ke maƙale da bango ko rufi, kuma ya ƙara da cewa idan babu maganaɗisu, ba sa iya kwanciya —“ko ina yana jan ka ƙasa.”

Wata tambayar da ta amsa ita ce, “Yaya tururin radiation a samaniya ke shafar tsatson halittar iri na noma?”

Ta ce radiation da ƙarancin maganaɗisu zai iya ƙaramin tasiri kan iri, wanda masana kimiyya ke nazari ta hanyar gwaje-gwaje. Wannan canje-canje za su iya buɗe sabbin hanyoyin kyautata ƙarfin iri a duniya.

Babban Daraktan hukumar NASRDA, kuma mai masaukin baƙi a taron, Dr. Mathew Adepoju, ya bayyana shirin a matsayin gagarumi.

Dr. Adepoju ya sha alwashin cewa NASRDA za ta ci gaba da samar da damarmakin ƙarfafa makarantu da ɗalibai don su zama masu gogayya a ƙasashen duniya.