Ana shirin farfaɗo da titin jirgin ƙasa mai tarihi na Hejaz Railway, lamarin da ke nuna farfadowar layin dogo na zamanin Daular Usmaniyya wanda ya a baya yake jigilar 'yan kasuwa da mahajjata daga Istanbul zuwa birane masu tsarki na Musulunci, Madina da Makka, da sauran wuraren da ke tsakanin su.
Turkiyya da Siriya da Jordan sun yi alkawarin gyara tare da zamanantar da titin, wani aiki da jami'ai da masana suka ce ba titin jiragen ƙasa kawai za a farfado ba har ma da tattalin arziki da sulhu a yankin.
A wani taron fasaha na ministocin sufuri da aka gudanar a birnin Amman a ranar 11 ga Satumba, kasashen uku sun amince su dauki “matakin farko mai ƙarfi” don farfado da titin.
Titin ya haɗe ƙasashen Turkiyya da Siriya da Jordan da Saudiyya, yana tafiyar tsawon kilomita 1,750, inda yake haɗe wasu daga cikin manyan biranen yankin.
Ministan Sufuri da Kayan More Rayuwa na Turkiyya, Abdulkadir Uraloglu ya ce Ankara za ta tallafa wa Siriya wajen kammala kilomita 30 na titin da ya ɓace, yayin da Jordan za ta binciki damar fasaha don gyaran injinan jirgin ƙasa da kuma yiwuwar amfani da injinan tarihi zuwa Damascus.
Farfesa Suay Nilhan Acikalin, ƙwararriya a harkokin dangantakar ƙasa da ƙasa daga Jami’ar Haci Bayram Veli da ke Ankara, ta ce sake bude titin Hejaz Railway ba kawai zai zama “wani karfi na tarihi ba ne, amma kuma wani abin da zai kawo ci gaba da hadin-kai a yankin.”
“Farfadowar titin Hejaz Railway yana da matuƙar mahimmanci ga yankin,” ta shaida wa TRT World.
Taron Amman ya kuma samar da wani daftarin yarjejeniya don zurfafa hadin kai a harkar sufuri ta hanya, dogo da hanyoyin kayan aiki.
An yi tsammanin za a sanya hannu kan wannan takarda daga baya a wannan shekara a matakin ministoci.
Turkiyya za ta shirya cikakken shirin aiki kafin taron, tana bayyana matakai na zahiri da za a dauka don kungiyoyin fasaha na ƙasashe uku.
Daya daga cikin sakamakon da aka samu nan take shi ne yarjejeniyar dawo da sufuri ta hanya tsakanin Turkiyya da Jordan ta Siriya, wanda ya kawo ƙarshen dakatarwa na shekaru 13.
Minista Uraloglu ya kuma nuna mahimmancin dabarun hada Turkiyya kai-tsaye da Bahar Rum ta hanyar Tashar Aqaba ta Jordan, wani mataki da zai iya karfafa sarkokin samar da kayayyaki a Gabas ta Tsakiya da ma sauran duniya.
Mahimmancin dabaru
Acikalin ta sanya farfadowar titin dogo a cikin wani babban yanayin siyasa, tana jaddada duka alamar tarihi da kuma amfani na zahiri na wannan aikin.
“Wannan shi ne daya daga cikin ayyukan da suka zama gaskiya a cikin kokarin Turkiyya na shekaru uku da suka gabata—daga yaki da ta’addanci zuwa cimma burin ci gaba.”
“Baya ga Aikin Hanyar Ci Gaba tare da Iraki da kuma yiwuwar hanyar arewa ta Zangezur, wannan aikin yana wakiltar wani kokari mai fadi na ci gaba,” ta kara da cewa.
Acikalin ta jaddada cewa zaman lafiya a Siriya - bayan faduwar gwamnatin Asad - ya sanya cewa irin wadannan ayyuka za su yiwu.
“Wuraren da Hejaz Railway ya ratsa sun kasance cikin rikici a tsawon shekaru,” ta lura.
“Amma yanzu da Siriya ta shiga wani lokaci na kwanciyar hankali, yiwuwar farfado da wannan titin—wanda ke hade Iraki, Siriya, Turkiyya, da yankin gaba daya—ya zama mai yiwuwa kuma mai matukar mahimmanci.”
Farfesa Oktay Firat Tanrisever daga Jami’ar Fasaha ta Gabas ta Tsakiya da ke Ankara, ya jaddada mahimmancin dabaru da tattalin arziki na wannan aikin.
“Gyara da zamanantar da wannan titi mai tarihi — musamman hanyar Siriya–Jordan—zai sake bude wata mahimmiyar hanyar kasuwanci tsakanin Turkiyya da Bahar Rum,” ta shaida wa TRT World.
“Turkiyya za ta iya faɗaɗa kasuwancinta sosai da Saudiyya da Tekun Afirka, tana isar da kaya cikin sauri, amana, da kuma rage kudin sufuri,” ya ci gaba.
“Ga Siriya, wannan zai samar da sabbin hanyoyin kasuwanci da kuma ƙarfafa kasuwanci gabadaya tsakanin kasashen yankin.
Hadin kai a harkar sufuri tsakanin Turkiyya, Siriya, da Jordan ba kawai zai fadada damar shiga yankuna masu fadi ba, amma kuma zai karfafa zaman lafiya da ci gaba a yankin.”
Titin dogo mai tarihi da makoma
An bude Hejaz Railway a karon farko a shekarar 1908, an gina shi don hada Istanbul da Madina, yana saukaka kasuwanci da Aikin hajji.
A farkon kwanakinsa, titin ya dauki mahajjata a tafiyarsu zuwa biranen tsarki, yana hada al’ummomi masu nisa a cikin hamada da iyakoki.
An gina titin tsakanin 1900 da 1908 a karkashin Sarki Abdulhamid II na Daular Usmaniyya, yana hada Istanbul da birane masu tsarki na Makka da Madina, tare da tsawaita zuwa Damascus da wasu sassan Yemen.
Rushewarsa a lokacin Yakin Duniya na Farko ya bar manyan sassan titin a lalacewa, tare da tashoshin da suka rage da injinan jirgin kasa da aka ajiye a matsayin kayan tarihi fiye da kayan aiki.
Yanzu, tare da goyon bayan gwamnatoci da masana yankin, titin yana samun sabon hangen nesa a matsayin wani aiki da ke hada tarihi da makoma.
“Farfadowar Hejaz Railway ba kawai game da gyara titin karfe da dutse ba ne,” in ji Minista Uraloglu.
“Abu ne da ya shafi sake hada mutaneda, bude sabbin hanyoyin kasuwanci, da kuma gina makoma mai zaman lafiya da ci gaba a yankinmu.”
Da zarar an kammala, titin zai tsaya a matsayin wani abin tarihi da kuma hangen nesa na makomar yankin: wata hanyar dogo da ke tsallakawa daga Mashigin Istanbul zuwa Bahar Rum, kuma alama ce ta kasuwanci, hadin kai, zaman lafiya da ci gaba.