Tashin hankali ya ɓarke a garin Kukurantumi da ke Gabashin ƙasar Ghana bayan mutuwar wani mutum da ake zargi da ta’ammali da kayan maye a hannun 'yan sanda.
Lamarin ya haifar da ƙazamin artabu tsakanin mazauna garin da jami'an tsaro.
Rahotanni sun bayyana cewa matashin wanda aka tsare shi a caji-ofis mai suna Bright ya mutu ne bayan an kama shi a yayin wani samame da ‘yan sanda suka kai yankin, inda aka kama shi da wani abu da ake zargin tabar wiwi ne.
Mazauna yankin sun yi zargin cewa wani ɗan sanda mai suna Kumador ne ya lakaɗa masa dukan da ya yi ajalinsa.
A sakamakon haka ne, matasan yankin suka fusata kana suka kai farmaki ofishin ‘yan sanda na Kukurantumi a ranar Lahadi, inda suka riƙa jifan jami’an tsaro da duwatsu tare da neman a yi adalci.
Kazalika, matasan sun kai hari kan tawagogin rundunar ‘yan sandan yankin Gabas da ke yaƙi da ta’addanci da aka tura domin tallafa wa abokan aikinsu daga sashen Akyem Tafo tare da ƙona ofishin ‘yan sandan.
Tashin hankalin ya yi sanadin fasa gilasan motoci ƙirar Toyota Tundra (Registration GP 4004) da wata Toyota Hilux mallakin kwamandan rundunar ‘yan sandan yankin Gabas.
Haka kuma jami’ai biyu sun samu raunuka a ido yayin harin, an yi saurin kai su asibitin gwamnatin da ke Kukurantumi don samun kulawa.
Kawo yanzu dai 'yan sanda ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba, sai dai ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin mutuwar Bright.