Dama ta biyu don gyara fuskar yaro ɗan Kenya da ‘yan bindiga suka harba
AFIRKA
2 minti karatu
Dama ta biyu don gyara fuskar yaro ɗan Kenya da ‘yan bindiga suka harbaHarsashin da ‘yan bindiga suka harba a watan Disamban 2023 yayin da suka kai hari unguwar Meru ya samu Ian Baraka a mukamikinsa na kasa tare da fita ta tsakiyar fuskarsa.
Ana sa ran Ian Baraka zai dawo da yin murmushi bayan yin tiyatar. / Others
18 awanni baya

Likitocin fida a Kenya na shirin yin gyaran fuska da suka ce shi ne irin sa na farko ga wani yaro dan shekara shida da ya samu rauni a fuska bayan da wasu ‘yan bindiga sun harbe shi.

Harsashi ya samu Ian Baraka a muƙamuƙin kasa inda ya fito ta tsakiyar fuskarsa a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a gundumar Meru a watan Disambar 2023, a cewar rahotannin cikin gida.

Kwararru a asibitin Kenyatta na kasa sun ce yaron ya samu raunuka masu yawa a fuska da suka shafi iya numfashi, cin abinci da magana.

Sun ce za a yi wa yaron gyaran bangaren fuskar da ya cire wanda ake sa ran zai dawo da aikin sassan da abin ya shafa.

Ian ya riga ya yi gyare-gyaren naman fuska mai laushi kuma an shirya shi don fuskantar aiki mafi muhimmanci a ranar 25 ga Satumba.

"Kashi na farko na sake dawo da fuskar na nufin cewa dole ne mu ba shi wani abu da muke kira dashe na musamman ga marar lafiya don ba shi damar girma," Dr Andrew Okiariamu, wani likitan tiyatar fuska, ya shaida wa wani taron manema labarai.

"Wannan nau'in magani ne na kawo sabon cigaba saboda ba a taba yin irin sa ba a ga yaron da yake girma don bayar da ƙasusuwan su kara fadada, a yayin da kuma muke kokarin baiwa yaron ingantacciyar rayuwa.”

Dakta Margaret Mwasha, kwararriyar likitan hakora, ƙwararriyar gyaran haƙora, ta ce za a yi amfani da hanci da lebban silicon da titinium don maye gurbin wadanda ya rasa.

"Titanium wani abu ne wanda ya dace da kwayoyin halittar jikin mutum kuma an yi shi ta hanyar da kashi zai iya girma a cikin sa," in ji ta.

Abbas Gullet, shugaban gudanarwar asibitin, ya ce likitocin da suka dauki wannan aiki sun cancanci a karrama su saboda aikin samar da wannan hanya da babu irin ta sosai.

"Zai dauki lokaci, zai zama kalubale, amma sun rungumi kalubalen kuma sun ce za su iya, kuma ba a taba yin irin hakan a ko'ina a duniya ba, kuma abin da ya kamata mu yi murnar sa a matsayinmu na kasa kenan," in ji shi.