DUNIYA
1 minti karatu
Yankin Kerala na India na fama da wata cuta da ke cinye ƙwaƙwalwa
Ana kamuwa da cutar ‘Naegleria fowleri’ da ba a saba gani ba a wuraren ninkaya marasa tsafta, wuraren wasan ruwa da sauran wuraren nishadi.
Yankin Kerala na India na fama da wata cuta da ke cinye ƙwaƙwalwa
An bayar da sanarwa a jihar kudancin India bayan samun labarin mutuwar mutane 19. / REUTERS
17 Satumba 2025

Mutane 19 sun mutu a jihar kudancin India ta Kerala a 2025 sakamakon kamuwa da cutar ‘amoebic meningoencephalitis’ (PAM) mai cinye ƙwaƙwalwa, in ji Kwamishinar Lafiya ta jihar Veena George.

George ta ce jimillar mutane 69 ne suka kamu da cutar a wannan shekarar.

Jihar ta bayar da sanarwar kar ta kwana a yayin da cutar ke yaduwa, tashar talabijin din jihar DD ta rawaito hakan.

Ana kamuwa da cutar ‘Naegleria fowleri’ da ba a saba gani ba a wuraren ninkaya marasa tsafta, wuraren wasan ruwa da sauran wuraren nishadi, in ji Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Amurka CDC.

Ana yawan kiran cutar da ‘Amoeba mai cinye kwakwalwa” saboda tana iya kama kwakwalwar tare da lalata jijiyoyi da fatar ƙwaƙwalwar, kamar yadda aka bayyana a shafin intanet na CDC.

Ba wannan ne karo na farko da aka fara kamuwa da cutar a jihar ba.

A shekarar 2016 aka fara samun bullar cutar a karon farko.

Sashen Kula da Lafiya na Kerala ya ce “an samu rahotannin kamu wa da PAM a nan da can a yankunan jihar da dama a shekaru 10 da suka gabata.”