AFIRKA
2 minti karatu
Kusan ɓauna 100 ne suka mutu yayin turmutsutsun guje wa zakuna a Gandun Dajin Namibiya
Dabbobbin sun dinga faɗowa daga saman wani tsauni zuwa cikin kogi, wasu kuma sun yi ta faɗawa kan juna, a cewar Ma'aikatar Yawon Buɗe Ido.
Kusan ɓauna 100 ne suka mutu yayin turmutsutsun guje wa zakuna a Gandun Dajin Namibiya
Nambiya na samun kuɗaɗe sosai a fannin yawon buɗe ido saboda tana da dabbobin daji sosai. / Reuters
3 awanni baya

Akalla ɓauna 90 ne suka mutu a ranar Talata yayin da suke gudun tsere wa zakuna a gabashin Namibia, in ji jami'an kula da namun daji.

Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 5:00 na safe (0300 GMT) a kusa da Kogin Chobe, a yankin gandun daji na Zambezi, wanda ke da wadatattun namun daji da rafuka, da dazuzzuka.

Zakuna ne suka raraki ɓaunayen daga maƙwabciyar ƙasar Botswana, kamar yadda mai magana da yawun Ma'aikatar Yawon Shaƙatawa, Ndeshipanda Hamunyela, ta shaida wa AFP.

"Wannan lamari ne mai ban takaici. Dabbobin sun faɗo daga wani tsauni mai tsawo zuwa cikin kogin, wasu kuma sun yi ta faɗawa a kan juna," in ji ta.

Bidiyon da aka wallafa a kafafen sada zumunta ta gidan talabijin na gwamnati, Namibia Broadcasting Corporation, ya nuna wasu maza kusan 12 suna amfani da gatari suna yanka naman ɓaunayen da suka mutu, suna lodawa a cikin motoci.

Namibia, ƙasa mai yanayin hamada a kudancin Afirka, tana samun kusan kashi bakwai cikin ɗari na tattalin arzikinta daga yawon shaƙatawa.

A shekarar 2018, fiye da ɓauna 400, wadanda ake zaton zakuna ne suka rarake su, sun nutse a wani kogi a arewacin Botswana.

Mutuwar ɓaunaye sakamakon faɗawa kogi ba sabon abu ba ne a wannan yanki, sai dai ba masu yawa irin haka ba ne suka faye faɗawa a lokaci guda.