Sabon nazarin WHO da ke shawartar a daina dukan yara da nufin gyaran tarbiyyarsu
RAYUWA
5 minti karatu
Sabon nazarin WHO da ke shawartar a daina dukan yara da nufin gyaran tarbiyyarsuA kasashen Afirka da dama an hana hukunta dalibai a makarantu, amma wani sabon nazari na WHO ya bayar da shawarar samar da dokoki tare da wayar da kai da yin nasiha don kawar da abinda ya zama matsalar duniya.
Kimanin kashi 70 na yara a Afirka na fuskantar hukunci da duka a lokacin da suke makaranta. Hoto: WHO/S. Becker / WHO
11 Satumba 2025

Daga Pauline Odhiambo

Har yanzu Michael Otieno yana tunawa da bulalar da aka yi masa. Ba kawai a hannunsa ba, amma a tunanin kansa.

A makarantarsa ​​ta firamare da ke yammacin Kenya, bulala ta zama ruwan dare kamar yadda allo ya zama.

"Idan ka makara, sai an yi maka bulala. Idan kuka manta aikinku na gida, sai a yi muku bulala.

“Ba batun koyarwa ba ne, ya zama sanya tsoro ne kawai," in ji wani akawu mai shekaru 32 mazaunin birnin Nairobi yayin tattauna wa da TRT Afrika.

"Wannan tsoron bai sa na zama dalibin da ya fi saura ba, ya sanya ni cikin damuwa, ya sa na yi imani cewa tashin hankali shi ne maganin farko na wata matsala. Ya ɗauke ni shekaru da yawa kafin na watsar da wannan ra’ayin."

Ba Otieno ne kaɗai ke dauke da tabon hukunci da bulala ba har zuwa lokacin da ya girma. A cewar wani sabon rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) mai taken - "Hukunta Yara: Tasirin Kiwon Lafiyar Jama'a" - azabtarwa ta jiki da sunan gyara yara ya zama ruwan dare gama gari kuma yana haifar da lahani mai ɗorewa ga lafiyarsu da ci gabansu.

Matsala gama-gari

Binciken ya nuna cewa kimanin yara biliyan 1.2 a fadin duniya suna fuskantar azabtarwa ta jiki a gida kowace shekara.

Kasashen Afirka ba a bar su a baya ba, yayin da iyaye suka bayar da rahoton cewa kashi 77% na yara a Togo da kashi 64% a Saliyo masu shekaru 2-14 na fuskantar hukunci a makarantu, kuma sakamakon ya samu ne wata guda kafin fitar da wannan rahoto.

Makarantu ma ba su fita daga wannan koma ba. Binciken ya nuna cewa kashi 70 cikin 100 na yara a fadin Afirka na fuskantar bulala a lokacin karatunsu na makaranta.

Etienne Krug, daraktan sashen tantance lafiya na WHO ya ce "Yanzu akwai kwararan shaidun kimiyya da suka nuna cewa hukunta yara na haifar da hatsari da yawa ga lafiyar yaran."

"Ba ya bayar da wata fa'ida ga halayya, ci gaba ko kyautata rayuwar yara, kuma ba wani amfani ga iyaye ko al'umma. Lokaci ya yi da za a kawo karshen wannan mummunar dabi'a."

Illa mai dawwamammiya

Rahoton na WHO ya yi cikakken bayani game da yadda yi wa yara bulala ko wani nau’in hukunci da ya shafi jiki ke haifar da cutar wa ga lafiyarsu, ciki har da yawaitar damuwa ga kwayoyin halitta da sauyi kan yadda kwakwalwarsu ke aiki.

Akwai shaida ta kimiyya da ke nuna cewa yaran da suka fuskanci irin wannan horon ba su da yiwuwar samun ci gaba da kashi 24% fiye da takwarorinsu waɗanda ba su fuskanci hakan ba.

Lamarin na shafar lafiyar kwakwalwa, tare da ƙarin hatsarin damuwa, tsananin damuwa da ƙarancin girmama kai waɗanda galibi suna dawwama har zuwa girma.

Ma’aikaciyar kula da yara Adeola Okonkwo, wacce ke aiki a Legas a Najeriya, tana shawartar iyaye akai-akai da su yi amfani da wasu hanyoyin da za su bi wajen ladabtarwa.

Okonkwo ta ce: “A koyaushe ana cece-kuce, ‘An yi min duka kuma na samu lafiya’. "Amma mun kasance?

Da yawa daga cikinmu suna ɗauke da raunukan ɓoye da ke nuna yadda muke saurin mayar da martani cikin fushi, rashin iya bayyana motsin zuciyarmu, da kuma zuzzurfar buƙatar aminta.

Muna cakuda girmama wa da tsoro. Muna karya ruhun 'ya'yanmu kuma muna kiran shi horo."

Rusa wannan ta’ada

Binciken na WHO ya tabbatar da abin da watakila ko da yaushe aka sani amma ba a kula da shi - cewa yaran da aka yi wa bulalar na zama manya da su ma suke yin hakan, suna mayar da illar ba komai ba.

Waɗannan yaran kuma an san su da nuna ɗabi'ar fada d abacin rai da yiwuwar yin tashin hankali ko aikata laifuka daga baya a rayuwarsu.

Duk da cewa da yawa daga cikin ƙasashen Afirka sun haramta ladabtar da yara a makarantu, binciken ya nuna cewa doka kawai ba ta isa ta kawar da imanin da ke da tushe ba game da yadda ya kamata a horar da yara a gida da kuma a aji.

WHO ta fayyace cewa dole ne a ƙara yin doka tare da gangamin wayar da kan jama'a da tallafin ƙwararru ga iyaye da malamai.

Ga mutane irin su Otieno, binciken ya zama ingantaccen abin da suka fuskanta amma sun sami wahalar bayyana halin da suka shiga saboda yanayin zamantakewa.

"Dole ne mu tambayi kanmu ainihin abin da muke koya wa yaranmu," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

"Shin muna koyar da su daidai ne ko kuskure, ko kuwa muna koya musu cewa karfi yana sanya wa a yi rigima?

Ƙawo karshen wannan ba wai rashin mutunta al'adunmu ba ne; yana nufin zabar makoma mai kyau, mafi tsafta ga al’ummu masu zuwa. Ilimin kimiyya ya bayyana a fili. Cutar da gaske ce. Yanzu ne lokacin kawar da matsalar."

Rumbun Labarai
Dalilin da ya sa faɗuwar jarrabawa watakila batun tsari ne ba na ɗalibi ba
Kunkuru Jonathan: Dabba mafi tsufa da ya kwashe shekaru 193 a duniya
Gaskiya mai ɗaci: Yadda rashin haraji mai yawa kan lemuka da giya ke illata lafiyar mutanen Afirka
Aden Abdullahi: Wani matashi da ke kula da dabbobin da ke gararamba a kan titi
Kenya na jimamin mutuwar toron giwa mai babban haure, da ya shekara 54 a duniya
Wani ɗan Nijeriya, Fado the Great yana ƙoƙarin maido da tashen wasan tsafi
Me ya sa dokoki ke gaza bayar da kariya ga matan da ake yi wa auren wuri kuma na dole
Waye ainihin wanda ya gano 'Victoria Falls', ɗaya daga cikin manyan kwazarin ruwa a duniya
Dabarun ƙara kaifin basirar yara
Me ya sa ba a iya yi mana bayanin wasu abubuwan da ke ba mu tsoro ba?
Dan Iraki mai zayyana ya kammala rubuta Kur'ani mafi girma da hannu a Istanbul
Batun auren Mai Wushirya da 'Yar Guda ya ja hankali a shafukan sada zumunta a Nijeriya
Jite Odeworitse: Attajirin Nijeriya ya janyo ce-ce-ku-ce sakamakon auren mata 19
Yadda ɗaliban Nijeriya suka samu zantawa da ‘yar-sama-jannati da ke Tashar ISS a sararin samaniya
Yadda dafa abinci na haɗin gwiwa a Somaliya ke ciyar da ɗaruruwan Falasɗinawa a Gaza
Hilda Baci: Fitacciyar mai girki ta Nijeriya ta dafa buhu 200 na shinkafa a yunƙurin kafa tarihi
Yadda ƙasaitaccen bikin 'yar hamshakin attajirin Nijeriya Femi Otedola, Temi ya ɗau hankali
Hotunan yadda dubban Musulmai a ƙasashen duniya suka yi murnar Maulidin Annabi
Ranar Hausa ta Duniya ta 2025 ta ƙayatar da gagarumin biki a Daura
Manufar bai ɗaya ta tsare harshe ta hade kawunan al’ummar Songhay-Zarma-Dendi