NIJERIYA
2 minti karatu
Hatsarin tankar dakon mai ya kashe aƙalla mutum 38 a Jihar Neja ta Nijeriya
Ganau sun ce waɗanda lamarin ya shafa suna kwasar man da ke gudana daga tankar man da ta faɗi ne a lokacin da lamarin ya haddasa gagarumar gobara da ta mamaye mutane.
Hatsarin tankar dakon mai ya kashe aƙalla mutum 38 a Jihar Neja ta Nijeriya
Fashewar wata motar dakon mai a jihar Nejar Nijeriya ta kashe aƙalla mutum 38 ranar 21 ga watan Oktobar shekarar 2025. / Reuters
14 awanni baya

Aƙalla mutum 38 sun rasa rayukansu yayin da mutum 40 suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai ranar Talata a Jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe a tsakanin ƙauyukan Ezzan da Badeggi inda wata motar dakon mai ta faɗi a kan hanyar Bida zuwa Agaie a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar.

Ganau sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Anadolu cewa mazauna yankin sun garzaya inda tankar ta faɗi domin kwasar man da ke zuba daga motar. Kuma ba da jimawa ba tankar ta kama da wuta.

Da yawa daga cikin mutanen sun ji rauni iri-iri kuma a halin yanzu suna samun kulawa a asibitin Badegi da kuma asibitin Ezza.

Aikin ceto

“Yawancin waɗanda lamarin ya rutsa da su su ne masu kwasar man da ke zuba daga tankar da ta faɗi kafin ta kama da wuta,” kamar yadda shugaban ƙungiyar direbobin dakon mai ta Jihar Neja, Farouk Mohammed Kawo, ya shaida wa manema labarai.

Hajiya Aishatu Sa’adu, kwamandar hukumar kiyaye haɗɗura ta FRSC, a Jihar Neja, ta ce “har yanzu jami’ansu suna gudanar da aikin ceto a inda lamarin ya auku. Iftila’in ya janyo cunkoson motoci a kan titin da ke da yawan masu zirga-zirga.”