| Hausa
RAYUWA
5 minti karatu
Dalilin da ya sa harshenku na asali ke tsara duk wani yare da kuke magana da shi
Sautin da muke ji da kuma koya a lokacin yarinta na tsara ire-iren kalmomin da muke furtawa a tsawon rayuwarmu, suna gina tushen harshen mutanen da suka ƙware wajen iya yaruka da yawa wato 'polyglots'.
Dalilin da ya sa harshenku na asali ke tsara duk wani yare da kuke magana da shi
Kowanne harshe na tsara yananin kalmomin da baki ke furtawa ta hanyoyi daban-daban / TRT Afrika Hausa
2 awanni baya

Jean-Christophe Mbang ya iya managa da harshen Faransanci da Bassa cikin sauƙi, sai dai wani abun lura shi ne, duk lokacin da ya yi magana da Faransanci za a ji harshensa na asali na Kamaru ya fito, kamar idan zai ce "lé" maimakon "le" - wani ɗan sauti ne ke fitowa wanda ke bayyana harshensa na asali.

A harshen Bassa, sautin harafin "e" ya yi daidai da "é", kuma haka sautin harafin yake a sauran harsuna, yana fito da abin da zai iya kama da kuskuren nahawu amma a zahiri shaida ce ta wani abu mai muhimmanci game da yadda muke koyon iya magana.

Ƙalubalen da Maryam ke fuskanta daban ne, matar wadda ‘yar asalin Aljeriya ce takan iya sarrafa harufan Larabci masu rikitarwa wajen magana, amma furta sunayen Faransanci kamar Pierre ko Patrick na mata wuya. Harshen Larabci ba shi da harafin "p". Babu harafin a cikin harshen kwata-kwata, babu sautinsa, wanda hakan ke nufin babu wata hanya mai sauƙi da za a iya furta kalmomin da aka gina a kusa da shi.

Ba kurakurai ko gazawa ba ce, suna nuna ainihin yadda kowanne harshe yake: wato kowanne harshe yana horar da baki ta hanya daban, kuma yanayin salon magana na farko suna bin mu ne har tsawon rayuwarmu, kuma komai yawan harsunan da za mu koya daga baya.

"A fannin sauti, kowanne harshe yana da irin nasa sautin harufa na musamman da ke jaddada abin da mai magana ke ƙoƙarin isarwa," masanin harsunan Gabon Régis Ollo Nguema ya shaidawa TRT Afrika cewa "hakan shi ke bambanta harsuna."

Ya bayyana cewa, an gina harshe ne daga jerin sautuka, waɗanda masana harsuna ke kira tushen magana. Wannan tushe, wanda aka kafa tun mutum na yaro, yana ƙayyade ba kawai abin da za mu iya furtawa cikin sauƙi ba, har ma abin da ke da matukar wahalar furtawa sosai.

Sauya sauti

Alal misali Wolof, harshen da ake magana da shi sosai a ƙasar Senegal. Idan Moustapha, wanda ke zaune a yankin birnin Thiès na Senegal na so ya ce Mota da harshen Wolof sai, yace "wetir" a Faransanci kuwa, zai ce "voiture".

Kalmar "civilisé" ta kan koma "silwissé." "Lavabo" kuma "lawabo." kuma duk hakan ba kuskure ba ne ko kuma kwaikwayon wani abu ba. Harshen Wolof ba shi da sautin harafin ‘‘v’’ ko ‘‘c’’, don haka yana daidaita kalmomin aro daga Faransanci don dacewa da tsarin sautin haruffansa, yana canza yadda ake furta su da kuma yadda ake rubuta su.

Baturke na nuna irin wannan ƙa’ida ta wata hanya daban. Haruffansa 29, babu sautin "w," "x," ko "q." Mai magana da harshen Turkanci wanda bai taɓa koyon harshen Turanci ko Faransanci ba zai iya samun suna kamar "Malcolm X" da wahalar furtawa, akwai yiwuwar ya iya cire harafin ƙarshe baki ɗaya.

Duk da haka, mutumin da ya iya magana da harsuna da yawa zai iya dogara kan sautin haruffan da ya koya daga wasu harsuna don ya furta shi daidai.

Wannan tsari yana zama a bayyane musamman a sharhin wasanni, inda masu gabatar da shirye-shirye da ba 'yan Afirka ba ke yawan kuskure wajen furta sunaye daga nahiyar.

"Idan aka kwatanta da sunayen ‘yan Faransa ko wasu ƙasashe, zan iya furta sunan (Kylian) Mbappé daidai daga mahangar Afirka," in ji Nguema. inda ya yi ƙari da cewa "Zan iya cewa Mbaye ko ma Ndutumu. Mai magana da harshen Faransanci na asali zai furta su da M’bappé, M’Mbaye, ko N’dutumu."

Bambancin ya ta'allaka ne kan sautin haruffan da ake furta su ta hanci waɗanda ke bayyana kafin na baki. Masu magana da harshen Faransanci za su iya faɗin "mb" cikin sauƙi a cikin kalma kamar tombe, amma sau da yawa suna ganin yana da wahala su samar da irin wannan sautin a farkon kalma. Saboda ba su koyi wannan salo da tsari a lokacin ƙuruciyarsu ba.

Dawwamamman tsari

Yawan nazarce-nazarce da bibiya akai-akai suna taimaka wa mutane su koya har ma su ƙware wajen magana da harsuna da yawa, amma ƙwararru a fannin sautin haruffa sun yarda cewa ba za a iya shigar da wasu sautuka ba cikin kundin tsarin magana na mutanen da suka manyanta ba. Wasu za a iya kimanta su, sai dai a mafi yawan lokuta suna ɗauke da lafazi wanda ke nuna asalin inda mutum ya fito.

"Misali, a matsayina na ɗan Gabon, ba zan iya samar da nau'in sautukan haruffan da ake amfani da su a wasu harsunan Afirka ta Kudu ba," kamar yadda Nguema ya shaida wa TRT Afrika. Yana mai ƙari da cewa "tushen maganata ya ginu ne daga harsuna biyu - wato Fang da Faransanci. Zan iya furta sautin haruffan harshen Faransanci da kyau ba baifi, amma harshe na Fang ya fi nuna asalina."

Akwai harsuna kusan 7,000 a faɗin duniya, sai dai babu wani mutum ɗaya da zai iya koyon dukka tsarin sautin haruffan da ake da su. Har da Ziad Youssef Fazah, ɗan asalin Lebanon wanda ya ƙware wajen magana da harsuna 58, zai yi wuya ya iya karawa kan harsunan da ya riga ya sani a yanzu.

Ko bayan shekaru da yawa na koyo, kalmomin da muke ɗauka a matsayin "daidai" wajen furtawa suna da alaƙa da sautukan farko da muka koya a lokacin ƙuruciya waɗanda ke tasiri rayuwarmu ta har abada.