Ana samun ƙarin rarrabuwar kawuna a cikin gwamnatin Isra’ila ta haɗaka game da yadda ya kamata ƙasar ta mayar da martani ga yadda ƙasashe ke amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta, in ji rahotanni daga kafofin watsa labaran Isra’ila.
Firaminista Benjamin Netanyahu ya kira wani zama na gaggawa daga farko ba tare da Ministan Tsaron Ƙasa Itamar Ben-Gvir ko kuma Ministan Kuɗi Bezalel Smotrich ba, domin tattauna martanin Isra’ila ga matakan da ƙasashen suka ɗauka, kamar yadda kafar Channel 12 ta ruwaito ranar Lahadi.
Majiyoyi na siyasa waɗanda ba a bayyana su ba sun shaida wa kafar cewa, abokan Ben-Gvir suna ganin matakin a matsayin wani ƙoƙari na tausasa kiran da ake na faɗaɗa ikon Isra’ila zuwa Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Su da sauran masu ra’ayin riƙau suna neman tsauraran matakai ciki har da gaggauta shirin karɓe ikon da kuma rusa gwamnatin Falasɗinawa.
Sai dai kuma an ce Netanyahu ya fi son a ɗauki mataki na taka-tsantan, yana mai neman ɗorewar gwamnatin haɗakar da kuma kauce wa matsalar diflomasiyya.