Ra'ayi
SIYASA
10 minti karatu
ICC: Yaudara daga wadanda suka kafa ta, mafaka ga mambobin ƙasashen Afirka
Kotun ICC na da kasashe mambobi 125, ciki har da 33 na Afirka, inda take da hedikwata a Hague, Netherlands.
ICC: Yaudara daga wadanda suka kafa ta, mafaka ga mambobin ƙasashen Afirka
Kotun ICC da ke hukunta manyan laifuka / AP
29 Satumba 2025

A ranar 17 ga Yulin 1998, wakilai daga ƙasashe 160 sun yi taro a Roma, ƙasar Italiya, don kammala samar da dokar da za ta kafa Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya.

Duk da cece-kuce da aka yi, a karshe taron ya amince da yarjejeniyar Rome, inda kasashe 120 suka kada kuri'ar amincewa, bakwai suka ki amincewa, sannan 21 suka kaurace.

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) za ta kafu da zarar kasashe 60 sun amince da yarjejeniyar. Kodayake an fara tsara dokar a Roma, daga baya aka gyara ta a shekarun 1998, 1999, da 2000.

An kafa kotun a hukumance a watan Janairun 2002, bayan kasashe 60 da sun rattaba hannu kan yarjejeniyar, 22 daga cikinsu daga Afirka, sun amince da yarjejeniyar.

A yau kotun ta ICC tana da kasashe 125 da suka hada da kasashen Afirka 33, tare da hedikwatarta a birnin Hague na kasar Netherlands.

Tunanin kafa kotun ta ICC ya samo asali ne bayan da aka kafa kotunan laifuka na musamman da na wucin gadi da dama bayan yakin duniya na biyu don gurfanar da masu aikata laifukan yaki, da kuma kotuna a shekarun 1990 da 2000 wadanda suka shafi laifukan yaki da kisan kiyashi a Saliyo, Rwanda, da tsohuwar Yugoslavia.

An ƙirƙiri kotun tare da goyon bayan ƙasashen yammacin Turai, Canada, da Australia, an kafa kotun ta ICC a matsayin kotun dindindin don yin shari'ar mutanen da ake zargi da manyan laifuffukan da suka shafi duniya, wato kisan kiyashi, laifuffukan cin zarafin bil’adama, laifuffukan yaƙi, da laifin wuce gona da iri, da nufin kawo ƙarshen fin karfin fuskantar hukunci da kuma yin adalci ga waɗanda abin ya shafa.

Tarayyar Turai ta yi kakkausar suka kan zama mamba ta ICC ta yadda a cikin shekarun 2000 ta yi barazanar yanke huldar da ta hada da bayar da taimako ko sharadi, da kasashen Afirka da suka ki shiga yarjejeniyar.

Jim kadan bayan kafuwar ta, kotun ta ICC ta fara karbar shari'o'i daga Afirka. Har zuwa kwanan nan, fiye da kashi 90% na shari'o'in da kotun ta gudanar sun samo asali ne daga nahiyar.

Shugabannin kasashen Afirka biyu, shugaban kasar Sudan na lokacin Omar al Bashir, da shugaban kasar Kenya, tare da mataimakinsa William Ruto (wanda a yanzu shi ne shugaban kasar Kenya), sun fuskanci gurfanarwa a gaban kotu bayan fitar da sammacin kama su.

Daga baya an wanke su, amma shari'ar tasu ta haifar da fusata a Tarayyar Afirka, lamarin da ya janyo suka da kiraye-kirayen ficewar kasashen Afirka gaba daya daga kotun ta ICC.

Watakila shari'ar da ta fi jawo cece-kuce, wadda ta kara dagula shakku a tsakanin 'yan kasashen Afirka da dama game da kotun, ita ce ta Ivory Coast, wadda ba ta rattaba hannu a kai.

A cikin wannan lamari, an gurfanar da zababben shugaban kasar Mr. Laurent Gbagbo a gaban Hague tare da tsoma bakin sojojin Faransa da ke kasar, sai dai a shekarar 2019 aka wanke shi.

A gefe guda kuma, tunda aka kafa kotun ta ICC a shekara ta 2002, an aikata manyan laifuka na cin zarafin bil adama, laifuffukan yaki, da laifukan wuce gona da iri a kasashe mambobi irin su Birtaniya a lokacin da ta mamaye kasashen Afghanistan da Iraki.

Sai dai kotun ta kasa gudanar da bincike kan wadannan laifuffuka, da kuma wadanda Amurka, da Isra'ila, da Syria, da Sri Lanka, da sauransu suka aikata.

Misali, dangane da Isra’ila da ake zargi da wariyar launin fata da take hakkin dan Adam, Kotu ba ta dauki wani mataki ba har sai watan Nuwambar 2024, lokacin da ta bayar da sammacin kama Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, da tsohon Ministan Tsaronsa, Yoav Gallant.

A baya dai jami’an Isra’ila sun tursasa tsohuwar mai shigar da kara ta kotun ICC Fatou Bensouda da iyalanta, yayin da Amurka ta kakaba mata takunkumi tare da hana ta shiga kasar.

Amurka ta ci gaba da kakaba takunkumi kan masu shigar da kara da alkalan kotun hukunta manyan laifuka ta ICC a halin yanzu saboda binciken da ake yi kan zargin Isra'ila ta aikata laifukan yaki.

Shi ma shugaban ICC na yanzu, Mista Karim Khan, ya fuskanci barazana daga wadannan kasashe a fili ta kafafen yada labarai da kuma a boye ta hanyoyin diflomasiyya.

A cikin wata hira da CNN ta 2024, ya bayyana cewa wasu shugabannin Turai sun gaya masa a asirce cewa "An ƙirƙiri ICC ne don gurfanar da 'yan daba kamar Putin da 'yan Afirka."Wannan ya tabbatar da labarin wasu fitattun jami'an diflomasiyyar Afirka da suka kira kotun ta ICC a matsayin "cibiyar sabon mulkin mallaka".

Tun daga ranar 8 ga Oktoban 2023, Isra'ila ta fara aiwatar da abin da mutane da yawa suka kwatanta a matsayin kisan kiyashi na farko da aka watsa ta talabijin a tarihin dan Adam. Laifukan yaki da Isra'ila ke ci gaba da yi sun fallasa munafurcin kotun ICC da yawancin kasashen Turai.

Ban da wasu kalilan, irin su Spaniya, Ireland, da Norway, galibin kasashen Turai na ci gaba da muhawara kan ko Isra’ila na aikata kisan kiyashi, har ma ta kai ga kalubalantar ma’anar kisan kare dangi kamar yadda aka tsara a yarjejeniyar Rome.

Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 70,000, musamman mata da yara, a Gaza, yayin da take lalata duk wani abu mai mahimmanci ga rayuwa, da suka hada da makarantu, asibitoci, wuraren zama, tsarin ruwa, sadarwa, da samar da makamashi, kuma duk ana nuna wa a talabijin.

Ba da daɗewa ba bayan 7 ga Oktoba, maganganun kisan kiyashi sun yi yawa a cikin ƙasar. Har zuwa matakin shaidantar da Falasdinawa ministan tsaro na lokacin Gallant yana kiran su da "dabba a siffar mutum".

Jami'an Isra'ila, jami'an diflomasiyya, mambobin majalisar Knesset da majalisar ministoci, sojoji, kafofin watsa labarai, da kuma fararen hula da dama suna tada maganganu na nuna kiyayya da kira da a kawar da Falasdinawa da kuma mamaye kasarsu, har ma da amfani da yunwa a matsayin makami.

Amma duk da haka, mutane biyu ne kawai aka bayar da sammacin kama su, yayin da akasarin wadanda ke da hannu a kisan kiyashin ke ci gaba da yawo ba tare da an hukunta su ba.

Kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a Gaza ya bayyana hakikanin fuskar Turawa da suka taba yin kira g da a yi aiki da kotun ta ICC.

Kasancewar Turai na ɗaya daga cikin manyan masu bayar da gudunmawar kuɗi ga kotun ta ICC,  sun yi tasiri sosai wajen zubar da mutuncin kotun, inda wasu ke kiran ta da son zuciya ko kyamar Yahudawa, har ma ƙasashe kamar Hungary sun janye daga kotun.

Kafofin watsa labaran Isra'ila suna da hannu a kisan kiyashin kuma dole ne su dauki alhakinsu, yayin da kafofin watsa labarai na yammacin Turai kuma suka taka rawa ta hanyar haifar da ƙiyayya da kuma bayyana Falasdinawa a matsayin ƙananan ‘yan adam don sake fayyace laifukan cin zarafin bil'adama.

Dukkanin gwamnatocin Amurka na da (Joe Biden) da na yanzu (Donald Trump), tare da jami'an diflomasiyya, da yawa daga kasashen Turai, ciki har da Birtaniya da Faransa, da kuma Canada da australia na da cikakken hannu ko wani bangare a kisan gillar da ke gudana a Gaza ta hanyar samar wa Isra'ila hanyoyin da suka dace, kariyar diflomasiyya, makamai da taimakon kudi don aiwatar da kisan kiyashin.

Jami’an Isra’ila da ke da alhakin kisan kiyashin da suka hada da Gallant da Netanyahu, na ci gaba da yawo cikin walwala a fadin duniya, har zuwa kasashe mambobin kotun ICC, ba tare da fargabar kama su ba, lamarin da ya sanya amincewar kotun a duniya cikin wani yanayi na sarkakiya.

Wani abin al'ajabi shi ne yadda kasashen yammacin duniya suka yi kakkausar suka dangane da bukatar a kama shugaban kasar Rasha Putin, a wannan karon suna fafutukar ganin ba a kama Netanyahu da Gallant ba idan sun ziyarci kasashensu.

Kamar yadda aka nuna a sama, ICC ba ta nuna son kai kuma ta ɗauki tsarin gudanar da adalci. A baya dai Burundi ce kawai ta fara fice wa daga kotun; amma a baya bayan nan kasashen Afirka uku; Mali, Burkina Faso da Nijar, sun sanar da ficewa daga kotun ta ICC saboda wasu dalilai da aka ambata a baya.

Sun bayyana cewa "ICC ta tabbatar da kanta ba ta iya aiwatarwa da kuma gurfanar da wadanda aka tabbatar da laifukan yaki, laifuffukan cin zarafin bil'adama, laifuffukan kisan kiyashi, da laifukan ta'addanci."

Tun da farko, a shekarar 2013, tsohon Firaministan Habasha, Hailemariam Desalegn, ya bayyana kotun ta ICC a matsayin "kotun farar fata," yayin da tsohon shugaban kungiyar Tarayyar Afirka Mr. Jean Ping ya kira kotun ta ICC a matsayin "kayan mulkin mallaka wanda aikinsa shi ne gurfanar da shugabannin Afirka da ke kan karagar mulki, da kashi 70% na kudadenta na zuwa ne daga Tarayyar Turai".

Kotun ta ICC tana aiki ne cikin sarkakiya, wanda ke sa yin adalci ga wadanda abin ya shafa yana da wahala. Ana iya bayar da rahoton laifuka kawai don bincike idan wani ɗan wata kasa ya kai kara kotu, wanda aka aikata a cikin yankin kasar, a cikin kasar da ta amince da hurumin Kotun, ko kuma ta hanyar samun shigar da korafi daga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya (UNSC).

Wannan tsarin yana da iyakantacciyar damar yin adalci ga yawancin wadanda abin ya shafa. Wani batu kuma shi ne wadanda ake zargi da bayar da umarnin aikata laifuka a karkashin dokar Rome ne kadai za a iya gurfanar da su a gaban Kotu, yayin da masu aikata laifukan kai tsaye ke da kariya daga gurfana a gaban kuliya.

Bugu da ƙari, kasashen biyar mambobin dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun gurgunta ayyukan Majalisar, wadanda su ne ke cewa a yi ko kar a yi Sakamakon wannan tsari, ba a gudanar da bincike kan laifukan yaki da cin zarafin bil adama da aka aikata a Syria da Yemen, inda aka kashe sama da mutane miliyan guda.

Don haka ya kamata Tarayyar Afirka ta dauki wani kuduri na dakatar da hadin gwiwa da kotun ta ICC, ko dai a gaba daya ko a wani bangare, da kuma nuna goyon bayan ficewar kasashen Afirka daga kotun.

Saboda kotun ICC ta keta hurumin Tarayyar Afirka tare da kawo cikas ga yunkurin kungiyar na warware rikice-rikice.

Ya kamata AU ta kuma mayar da hankali kan karfafa tsarin adalci na cikin gida a tsakanin kasashen Afirka, da tabbatar da cewa za su iya dakile laifukan yaki da cin zarafin bil'adama a nan gaba.

Ta wannan hanyar, za a iya yin adalci ga wadanda abin ya shafa, kuma maimakon neman adalci a kasashen waje, 'yan Afirka za su iya dogaro da tsarin cikin gida wanda ke kare rayukansu da dukiyoyinsu.

A ƙarshe, kotun hukunta manyan laifuka da aka kafa a ƙarƙashin Tarayyar Afirka za ta kasance mafi manufa da matsayi mafi kyau don tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa fiye da ICC, wadda ke wajen nahiyar.

Kafa Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Afirka, wanda a yanzu ya zama babu makawa sai an yi hakan, zai kawo gaskiya da adalci a Tarayyar Afirka.

A matsayinta na babbar hukumar da ke da alhakin tinkarar kalubalen nahiyar, dole ne a baiwa kungiyar ta AU ikon gurfanar da 'yan Afirka da suka aikata munanan laifuka na cin zarafin bil'adama.

Irin wannan kotun za ta karfafa karfin AU na tafiyar da harkokinta da tabbatar da adalci a cikin Afirka.

Marubucin, Ali Mohamed Farah,  dalibin digiri na uku ne a fannin kimiyyar siyasa a Cibiyar Nazarin Zamantake ta Jami'ar Ankara Yıldırım Beyazıt, kuma dan kasar Djibouti.

Togaciya: Ba lallar ra’ayin da marubucin ya bayyana ya zama ya yi daidai da ra’yoyin dab’i na TRT Afrika.