Sarkin Qatar ya faɗa wa shugabannin duniya cewa ƙasarsa tana ci gaba da ƙoƙarinta na diflomasiyya don kawo ƙarshen yaƙin Gaza duk da mummunan harin Isra’ila kan shugabannin Hamas a ƙasar wadda ke yankin Gulf.
Da yake jawabi ga babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya a yammacin Talata, Sarki Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya yi tir da harin Isra’ila "na cin amana" a tsakiyar unguwannin mutane a birnin Doha, inda Hamas ke da ofishin tuntuɓa.
Ƙalubale kan diflomasiyya
Qatar, tare da Masar da Amurka, sun jagoranci ƙoƙarin samar da cikakken matakin tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas, inda aka gudanar da zagayen diflomasiyya a Doha, wanda bai yi nasara ba.
Ya faɗa wa Babban Zauren Taron cewa, "Saɓanin iƙirarin firaministan Isra’ila, wannan hari ba ya cikin halastaccen haƙƙin bibiyar masu ta’addanci" kuma ya "kassara ƙoƙarin diflomasiyya da ke muradin kawo ƙarshen kisan ƙare-dangi kan al’ummar Gaza".
Ya ƙara da cewa, "Za mu yi aikin diflomasiyya yayin da abokan gabarmu suke ganin sauƙin amfani da makamai".
"Za mu ci gaba da ƙoƙarinmu na haɗin-kai, tare da haɗin gwiwa da Masar da Amurka."
Kisan kiyashi
Sarki Al Thani ya zargi Isra’ila da amfani da yaƙi a matsayin makami don mayar da Gaza mara zaunuwa, inda take lalata gidaje, makarantu, asibitoci, da kayan more rayuwa don tilasta ƙauracewa.
Ya yi gargaɗin cewa wannan yaƙin ba a Gaza ya tsaya ba, inda ya alaƙanta shi da babban burin kankane Gaɓar Yamma, don sauya matsayar da ake da ita a Al-Aqsa Mosque, ɗaya cikin mafi darajar wurare ga Musulmai a duniya.
Ya ce ayyukan Isra’ila sun kai matakin kisan ƙare-dangi kuma ya nuna hujjar manufar tsarinta na “Faɗaɗa Ƙasar Isra’ila,” wanda ke sanya zaman lafiya ya ƙi yiwuwa" Manufarsu ita ce ruguza Gaza don su hana su rayuwa. Sakamakon haka, shugaban Isra’ila yana so ya ci gaba da yaƙi."
Amincewa da Ƙasar Falasɗinu
Sarkin Qatar ɗin ya kuma jaddada kiransa na kafa ƙasashe biyu bisa iyakokin 1967 da kuma sanya Gabashin Jerusalem a matsayin babban birnin Falasɗinu.
Ya yaba wa ƙasashen da suka riga suka amince da ƙasar Falasɗinu, yana mai cewa wannan matakin yana nuna ƙaƙƙarfan saƙon cewa: wannan matsanancin zalunci ba zai goge mataki nagari ba.
Ya nemi sauran ƙasashe su biyo sahu, kuma ya yi gargaɗin cewa yin shiru kawai yana ƙarfafa cigaba da kisan kiyashi ne da mamaya.
Tasirin Ƙasashen Duniya
Sarkin Qatar, Emir Al Thani ya bayyana Doha a matsayin amintacciyar mai shiga tsakani a faɗin duniya.
Ya yi nuni da rawarta a warware rikici, daga Ukraine zuwa Afirka, ciki har da ƙoƙarin samar da zaman lafiya a Jumhoriyar Dimukuraɗiyyar Congo.
Ya kuma sha alwashin tallafa wa neman daidaita lamura a Syria, Lebanon, da Sudan, inda kuma ya bayyana aikin Qatar na shirya taron tattaunawa ta hanyar manyan bukukuwa kamar na shekara mai zuwa, na bikin Social Development Summit da kuma yunƙurin karɓar baƙuncin Wasannin Olympics na 2036.
Ya ce, “Wasanni wata mahaɗa ce ta zaman lafiya da fahimtar juna.”