| hausa
WASANNI
2 minti karatu
Kofin Duniya na 2026: Curacao ta zama kasa mafi kankanta da za ta buga gasar
Kasar Curacao da ke yankin Amurka ta Tsakiya tana da al'umma kimanin 150,000, da kuma faɗin ƙasa da ya kai murabba'in mil 171.
Kofin Duniya na 2026: Curacao ta zama kasa mafi kankanta da za ta buga gasar
Curacao ta goge tarihin da Iceland ta kafa a FIFA
19 Nuwamba 2025

A karon farko a tarihinta, ƙasar Curacao ta samu damar zuwa gasar ƙwallon ƙafa ta Kofin Duniya ta FIFA 2026, wadda za a yi a ƙasashen Amurka, Canada, da Mexico a baɗi.

Ƙasar da ke yankin Amurka ta Tsakiya, ta buga wasa da Jamaica, inda suka tashi canjaras babu ci, wanda ya sa ta ƙare Rukunin B a saman teburi da maki 12 daga wasanni 6.

Curacao ƙasa ce ƙarama wadda al'ummar suka kai kimanin 150,000, da kuma faɗin ƙasa da ya kai murabba'in mil 171.

A yankin hukumar ƙwallo ta CONCACAF da ke Amurka ta Tsakiya, Curacao da Haiti da Panama ne suka samu cancantar zuwa yanzu.

Zuwan Curacao, na nufin cewa ta goge tarihin da Iceland ta kafa na zama ƙasa mafi ƙanƙanta da ta buga gasar, inda ta je gasar da aka yi a Rasha a 2018.

Daraja a FIFA

A yanzu dai Curacao ce ƙasa ta huɗu da za ta buga gasar ta baɗi a karon farko, baya ga Cape Verde, Jordan, da Uzbekistan.

A 2010 ne Curacao ta zama ƙasa wadda ke cikin daular Masarautar Netherlands, sakamakon kawo ƙarshen tsarin yankin Netherlands Antilles.

A yanzu haka, ƙasar na da daraja ta 82 a jerin ƙasashen duniya mambobin FIFA.

Ita kuwa Jamaica ta zo ta biyu a rukunin, kuma za ta ci gaba da gwada sa’arta a wasannin cike gurbi da za a yi Mexico.

Kocin Jamaica, Steve McClaren wanda tsohon kocin Ingila ne kuma tsohon mataimakin kocin Manchester United, ya ajiye aiki nan-take, bayan gazawar ƙasar.

Rumbun Labarai
Za a iya dakatar da Ronaldo buga wasanni biyu bayan ya samun jan kati
Kotu a Jamus ta goyi bayan danwasan da aka kora kan goyon bayan Falasdinu
Shugaban Barcelona ya gwale Messi kan yiwuwar komawarsa Barca
Hukumar ƙwallon ƙafar Sifaniya ta maye gurbin Lamine Yamal da Jorge de Frutos
Yves Bissouma: An kwashe wa danwasan Tottenham fam 800,000 daga asusun banki
Kocin Man United ya mayar wa Ronaldo martani kan sukar halin da kungiyar ke ciki
'Agent' ya saka wa dan wasan Tottenham bindiga a ka don ya tursasa shi
Tawagar Portugal za ta saka jesin karrama tsohon ɗan wasanta bakar fata
Mutum 41,000 daga kasashe 126 ne suka shiga wasan tseren sassarfa na Istanbul karo na 47
Yadda kwazon Yamal a filin wasa ya ragu saboda ciwon matsematsi
Da gaske ne Barcelona za ta nemi Victor Osimhen don maye gurbin Robert Lewandowski?
Kotu ta umarci Barcelona ta fito da takardun biyan dala miliyan 9 ga wani rafari
Yamal zai kashe $16m don sayen gidan da Pique da Shakira suka zauna
Mohamed Salah ya cire Liverpool daga shafukansa na sada zumunta bayan wasansu da Frankfurt
Osimhen, Salah, Hakimi: Jerin sunayen ‘yan wasan da ke takarar gwarzon shekara na CAF
‘Yan Nijeriya uku za su taka leda a Gasar Zakarun Turai ranar Laraba
Ronaldo ba zai je India buga wasan Al-Nassr da Goa ba
Alonso ya yaba wa Vinicius kan janyo wa 'yan wasan Getafe biyu samun jan kati
Messi ya jajanta wa tawagar Argentina bayan Morocco ta doke su, ta ɗaga Kofin FIFA U20
Morocco ta ɗauki kofin duniya na ‘yan ƙasa da shekara 20 bayan ta doke Argentina