Portugal ta yi rashin nasara ne a hannun Ireland da ci 2-0 kuma wannan ne wasa na farko da shahararren dan wasan ya samu jan kati, bayan ya yi wa kasarsa ta Portugal wasanni 220 a tarihi.
Alkalin wasan ya kori Ronaldo ne bayan ya yi wa dan wasan bayan Ireland Dara O’Shea gula yayin wasan neman zuwa Gasar Cin Kofin Duniya da suka buga a birnin Dublin ranar Alhamis.
Korar dan wasan da aka yi za ta iya jawo masa rasa damarsa ta buga wasan farko da Portugal za ta buga a gasar a shekara mai zuwa, idan kasarsa ta samu damar zuwa gasar.
Da farko alkalin wasan ya fara bai wa shahararren dan wasan katin gargadi ne kafin daga bisani ya duba bidiyon da yake taimaka wa alkalin wasa yanke hukunci, sannan ya ba shi jan kati kai-tsaye.
A karkashin dokokin hukumar FIFA, za a iya dakatar da dan wasa buga wasanni biyu idan ya aikata laifukan rashin da’a irin wanda Ronaldo ya aikata.
Ronaldo ya zargi Kocin Ireland Heimir Hallgrimsson kan cewa shi ne ya matsa wa alkalin wasa lambar har ya sauya matsayarsa daga katin gargadin da ya fara ba shi zuwa jan kati.
Sai dai kocin ya ce kuskure ne dan wasan ya ce shi ne ya ja aka ba shi jan kati, kocin ya ce laifin da ya aikata ne ya jawo masa jan katin kuma ya ce wani karamin kuskure ne da ya yi sila.











