Tsohon ɗanwasan Mainz ta Jamus, Anwar El Ghazi ya samu nasara a ɗaukaka ƙarar da ƙungiyar ta yi kan biyan sa diyya, sakamakon korar sa da ta yi a 2023.
Mainz ta kori El Ghazi ne ba bisa ƙa’ida ba, saboda kalaman nuna goyon bayan Falasɗinu da ya yi, bayan da Isra’ila ta fara kisan ƙare-dangi a Gaza a Oktoban 2023.
El Ghazi ya wallafa a Instagram cewa, "Wannan ba rikici ba ne kuma ba yaƙi ba ne. Wannan kisan ƙare-dangi ne da ruguza dukiya kuma muna kallon abin na faruwa a idonmu. Daga kogi zuwa teku, Falasɗinu za ta samu ‘yanci".
Mainz ta dakatar da shi bayan nan kuma ta fitar da sanarwa da ke iƙirarin cewa El Ghazi ya bayyana nadama, kuma ya ba da haƙuri kan kalamansa.
Sai dai cikin hanzari, El Ghazi ya sake wallafa wani saƙon, yana cewa bai yi “nadama" ko "nisanta kansa" daga kalamansa na farko ba.
Bayan wannan sa-in-sa, Mainz ta soke kwantiraginsa ita kaɗai, wanda ya kai ga ɗanwasan mai shekara 30 ya shigar da ƙara a kotun ƙwadago ta gundumar Palatinate.
Biyan diyya
Kotun ta ce soke kwantiragin El Ghazi a ƙarshen 2023 saboda kalamansa kan Falasɗinu a soshiyal midiya ba daidai ba ne, inda ta ce dole a biya shi cikakken albashinsa.
Tun a Yulin 2024 wata kotun ta tabbatar wa El Ghazi ‘yancinsa na furta albarkacin baki, kuma ta ce ‘yancinsa yana sama da dalilan da Mainz ta bayar na soke kwantiraginsa.
Ɗanwasan ɗan asalin Netherlands tsatson Morocco, ya samu diyyar euro miliyan 1.5, daidai da albashinsa daga Nuwamban 2023 zuwa Yulin 2024.
Sai dai bayan biyan nasa, Mainz daga baya ta ɗaukaka ƙara don neman ƙwato kuɗin, inda kuma a yanzu ta yi rashin nasara.
Bayan yin nasara a kotun ɗaukaka ƙara, El Ghazi ya wallafa saƙo a Instagram ranar Alhamis yana cewa, "Ina godiya ga kotunan Jamus kan yin adalci".
Ya ƙara da cewa, “Ba za ku taɓa iya rufe bakin Falasɗinawa da masu goyon bayansu ba. Muna son Falasɗinu!!!"
Anwar El Ghazi ya buga wa tawagar Netherlands wasa, kuma a halin yanzu yana buga wa Al-Sailiya SC ta Qatar. A baya ya buga wa Ajax, Lille, Aston Villa, Everton, da Cardiff.











