| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Isra'ila ta tura akwatuna ɗauke da 'ƙoƙon kawunan' Falasdinawa da 'gawarwakin mata' zuwa Gaza
Tsohon shugaban jam'iyyar Labour Jeremy Corbyn ya ba da cikakkane bayani na wani saƙon daraktan asbitin Al-Shifa game da tura gawarwakin da aka yayyaga.
Isra'ila ta tura akwatuna ɗauke da 'ƙoƙon kawunan' Falasdinawa da 'gawarwakin mata' zuwa Gaza
Corbyn ya ambato rahoton asibiti game da mika gawarwaki a tsakiyar takaddama. (Hoton Ajiya) / AP
7 awanni baya

Danmajalisa mai zaman kansa kuma tsohon shugaban jam’iyyar Labour Jeremy Corbyn ya bayyana wani labari mai sosa rai daga daraktan asibitin Al-Shifa a Gaza da aka yi wa ƙawanya, inda ya ba da cikakken bayani na yadda aka aike gomman akwatuna ɗauke da ƙoƙon kawuna da kuma gawargwakin wasu Falasdinawa da aka guntule wasu sassan jikinsu.

Corbyn ya bayyana wani saƙon da ya samu daga Dakta Mohammed Abu Salmiya, wanda ya ba da rahoton cewa sojin Isra’ila ta miƙa akwatuna 66 na gawarwakin mutane zuwa asibitin.

Corbyn ya ce ma’aikatan asibiti sun buɗe akwatunan inda suka sami ƙoƙon kawunan Falasɗinawan da aka kashe a lokacin kisan ƙare dangin.

Bugu da ƙari, Corbyn ya bayyana cewa akwatunan da aka sauƙen sun haɗa da gawarwakin mata wadanda suka nuna alamun an guntule wasu sassansu, lamarin da ya janyo zargin cewa an cire wasu sassan jikinsu.

"Yanad a wuya a siffanta wannan," a cewar Corbyn.

"Wannan shi ne abin da ke faruwa mutanen Falasɗinu. Wannan shi ne ƙalubalen lokacinmu."

Guntule sassan jiki

Ma’aikatar Lafiyar Gaza tatabbatar da miƙa gomman gawarwakin da ba za a iya tantance masu su ba ta hannun ƙungiyar ba da agajin gaggawa ta Red Cross (ICRC).

Jami’an lafiya a wurin sun ba da rahoton cewa wasu daga cikin gawarwakin sun nuna "alamun da ba a saba gani ba," ciki har da alamun tsagu na asibiti da ke nuna cewa akwai yiwuwar an guntule sassan jiki daga gawarwakin kafin a dawo da su.

Dr Abu Salmiya, wanda shi kansa a baya dakarun Isra’ila sun tsare shi, ya ba da rahoton cewa da yawa daga cikin gawarwakin ba za a iya gane ko su waye ba ne inda suka ƙunshi ƙoƙunan kawuna da ƙasusuwa kawai.