Ana raɗe-raɗin cewa za a iya sauya sunan filin wasan Barcelona daga "Camp Nou" zuwa "Leo Messi", saboda karrama tsohon ɗanwasan ƙungiyar mai farin jini.
A kwanan nan ne Messi ya ayyana burinsa na dawowa Barca wata rana, lokacin da ya kai ziyarar bazata filin Camp Nou da aka yi wa kwaskwarima.
Matsayin tauraron ɗanwasan a ƙungiyar ya kai ga shugaban ƙungiyar Joan Laporta, ya ayyana burin gina gunkin Messi a farfajiyar filin wasan mai tarihi.
Sai dai bayanai daga ƙungiyar na cewa a yanzu Barcelona ba ta da niyyar sauyawa filin wasanta suna don girmama Messi.
A halin yanzu dai Messi na buga wa Inter Miami ta Amurka wasa, kuma a baya-bayan nan ya sanya hannu kan sabuwar kwantiragi da ƙungiyar da za ta kai shekarar 2028.
Duk da ya bayyana burinsa na komawa, ƙungiyar ba ta da wani shirin kawo shi a nan-kusa.
Gwarzon Barca
A Barcelona dai, Lionel Messi wanda ɗan asalin Argentina ne ya kafa tarihin zamowa gwarzo a fannoni da dama a gabaɗaya tarihin ƙungiyar.
Messi ya ciyo wa Barca ƙwallaye 672 a wasanni 778, inda ya taimaka mata lashe kofunan La Liga 10, da na Zakarun Turai 4, da ma tarin wasu kofunan.
Sai dai a 2021, an tilastawa Messi barin ƙungiyar sakamakon rashin kuɗi, inda ya koma Paris Saint-Germain ta Faransa, kafin daga baya a 2023 ya koma Amurka da taka leda.
Amma fa har yanzu akwai masu tunani da burin ganin Messi ya koma taka leda a Barcelona, ko da a matsayin aro.
Duk da Messi na da shekaru 38, kasancewar yana ci gaba da samun tagomashi a filin wasa, ya sa ana sa ran zai ci gaba da wasa zuwa wasu shekaru masu zuwa.











