KASUWANCI
2 minti karatu
Hukumomi a Ghana sun kama mutanen da ake zargi da yin fasa-ƙwaurin zinari
Hukumomi sun fara kama Abdul Razak Seidu ne ranar 27 ga watan Agusta na shekarar 2025 da zinari da ya kai kilogiram 9.2 wanda kuɗinsa ya kai cedi miliyan 10.2.
Hukumomi a Ghana sun kama mutanen da ake zargi da yin fasa-ƙwaurin zinari
Ƙasar Ghana na gaba-gaba wajen samar da zinari a duniya / Reuters
17 Satumba 2025

Hukumar  da ke kula da hakar zinari a Ghana (Goldbod) ta kama mutum uku da ake zargi da yin fasa-ƙwaurin zinari da ya kimarsa ta kai cedi miliyan 100 daga ƙasar.

Da yake magana da manema labarai ranar Talata, shugaban hukumar Goldbod, Sammy Gyamfi, ya bayyana cewa mutanen suna cikin wata ƙungiya mai aikata laifuka da aka shafe makonni ana bincika tun lokacin da wani ɗan ƙasar ya fallasa ta ga hukumomi.

Mutanen da aka kama su ne: Abdul Razak Seidu da Bernard Nkrumah da Ibrahim Aremayew.

Hukumomi sun fara kama Abdul Razak Seidu ne a shataletalen Winnneba da ke Accra ranar 27 ga watan Agustan da ya gabata da zinari da ya kai kilogiram 9.2 wanda kuɗinsa ya kai cedi miliyan 10.2.

Binciken da aka yi daga baya ya sa an kama Benard Nkrumah, wani mai sayen zinari da ke da laisisi da yake aiki a kamfanin NK Bernak Enterprise, wani abokin kasuwancin Rafmoh Gold Ltd, wanda masu bincike suka yi imanin cewa shi ya ɗauki nauyin aikin gaba ɗaya.

“Wannan shi ne ƙurin zinari mafi girma da Goldbod ta taɓa bankaɗowa tun lokacin da aka kafa ta. Mun samu sammaci kuma muna sanya tukuicin cedi miliyan 1 kan ko wanne daga cikin mutum huɗu  da ake zargin domin a tabbatar da cewa an hkunta su,” in ji Sammy Gyamfi.

Dukkan waɗanda ake zargi da suke hannu an gurfanar da su a gaban kotu kuma an ba da belinsu, sai dai saura huɗun ana ganin suna ɓuya ne a wasu sassan Ghana da kuma ƙetare.

Goldbod ta yi alƙawarin bayar da tukuicin cedi miliyan huɗu ga duk wanda yake da bayani game da yadda za a kama mutanen huɗu da ake nema ruwa-a-jallo bisa zargin yin fasa-ƙwaurin zinari.

Mutane sun haɗa da Rafeeq Mohammed Nandoli wanda ake kira Salam da Muhammad  Afsal Puthalan da Abul Karim da Sadique Abubakari waɗanda ake nema ruwa-a-jallo bisa laifuka ciki har da fasa-ƙwaurin da safarar zinari ba tare da izini ba da kuma cinikin zinari ba bisa ƙa’ida ba.