12 awanni baya
Ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinu, Hamas ta miƙa ƙarin fiye da ‘yan Israila 13 da take tsare da su a Gaza zuwa ga Ƙungiyar Jin-ƙai ta Red Cross, cewar gidajen labarai a Isra’ila.
Rahotannin Channel 12 sun ce ranar Litinin ICRC ta karɓi fursunonin Isra’ila 13 daga reshen mayaƙan Hamas, Qassam Brigades, kuma a yanzu suna kan hanyarsu ta zuwa Isra’ila.
Za ku so karanta wadannan
Bayan miƙa fursunonin 13, an kammala sakin duka ‘yan Isra’ila 20 da ke raye, ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta, bayan an saki rukunin farko na mutum bakwai tun da fari a ranar Litinin.
An yi musayar tsararrun ‘yan Isra’ilan ne da fursunonin Falasɗinu 1,968, ciki har da 250 da aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai da rai, waɗanda za a saka ƙarƙashin yarjejeniyar ta Gaza.