An raba 'yan Sudan sama da miliyan takwas da matsugunansu: Hoto/Reuters

Daga Abdulwasiu Hassan

Tuna irin rayuwar da yake yi a baya ne kadai abin da Tijjani Musa ya mallaka.

Yana iya tuna kyawu da karamcin gidansa, dadin hira yayin cin abinci, da dukkan sauran jin dadi da ake yi a rayuwar yau da kullum.

Duk wadannan kafin 15 ga Afrilun 2023 ne. A yanzu da aka buga ƙugen yaki, aka bar gidaje babu kowa a fadin kasar Sudan, abin da ya rage a rusa shi ne ƙarfin halin miliyoyin farar hula na Sudan wadanda suka jure wahalhalu na tsawon shekara guda.

Tijjani ya fada wa TRT Afirka cewa "Kafin a fara yakin, muna da damar samun komai da muke bukata. Muna da gida da mota. Akwai ruwa da abinci da magunguna. Muna iya zuwa duk inda muke so. Muna iya sadarwa ga duk wanda muke so a kowanne lokaci."

Shi da iyalinsa na zaune a unguwar Ombada ta yankin Omdurman har zuwa lokacin da aka fara yakin tsakanin sojojin Sudan da mayakan RSF, wanda yakin ba iya raba su da matsugunansu ya yi ba, ya kacalcala su.

Suna cikin kusan 'yan kasar Sudan miliyan tara da aka raba da matsugunansu, kuma suke jiran samun mafita.

Sudan kasar da take da Musulmai mafiya rinjaye, kuma wadanda aka raba da matsugunansu sun yi azumin Ramadhan a cikin yaki. Hoto/GettyImages

Hasashe daban-daban da aka yi, sama farare hula 12,000 ne aka kashe a musayar wutar da aka yi a shekara dayan da ta gabata.

"A yanzu muna zaune a wajen Ombada a wani yanki da ake kira Sijnilhuda, wanda kamar kurkuku yake," in ji Tijjani.

"Shekara guda kenan da fara yakin, mun tsira da rayukanmu amma muna ci gaba da fuskantar matsaloli na samun muhimman kayan amfani. Babu zaman lafiya a rayuwarmu."

Yankin da Tijjani da sauran mutane da yawa ke fakewa na karkashin kulawar sojoji, watakila dalilin da ya sanya aka samun dan zaman lafiya kenan sama da Ombada.

Ya yi bayanin cewa "A unguwarmu, za a iya dukanka a tumurmusa ka. Mun samu hutu na duka da ƙarar bindigogi, da tsoron za a iya kai maka hari."

Iyalai da aka tarwatsa

Duk da cewa dan zaman lafiyar da ake da shi a Sijnilhuda ya ba shi dan hutun zuci daga tsoro a koyaushe na iya fuskantar hari, har yanzu Tijjani na fama da rashin ganin wasu daga iyalinsa.

Kimanin 'yan Sudan miliyan biyu sun gudu kasashe makota mafiyan su zuwa Chadi. Hoto/Reuters

Ya fada wa TRT Afirka cewa "Duba da yadda rayuwa ba ta da dadi a nan, wasu daga cikin yarana sun tafi Masar da Libiya." ya fada wa TRT Afirka.

Sadarwa tare da su a koyaushe ya zama kalubale saboda sashen sadarwa na Sudan ya shiga tasku saboda yakin da ake yi.

Tun bayan fara fadan, bangarorin da ke rikici da juna sun yi amfani da karfi wajen katse sadarwar intanet a matsayin makamin hana yaduwar bayanai a yankunan da suke rike da su.

Access Now, wata kungiya da ke neman tabbatar da hakkokin samun yanar gizo ga kowa, na kallon wadannan ayyuka a matsayin mai hana 'yan kasa hakkokinsu.

Amnesty International ma, ta yi kira da a kawo karshen katse hanyoyin sadarwar yanar gizo a kasar da yaki da tagayyara, tana cewa irin wannan abu na hana gudanar da ayyukan jinkai.

"Wannan bakin yanayin da ake ciki na shafar jamar da dama aka riga aka raunata da suke kokarin jure hari na tsawon shekara guda," Amnesty Unternational ta rawaito Sarah Jackson, mataimakaiyar daraktan shiyya na Gabashi da Kudancin Afirka, na fadin haka a watan Maris.

Ya ce "Ba tare da sadarwa ba, ayyukan jinkai da na gaggawa ba za su yiwu yadda ake so ba, za ma a dakatar da su gaba daya ne wanda hakan zai jefa rayuwar miliyoyin jytane cikin hatsari."

Kamar Tijjani, wani dan kasar Sudan Yaasir Ibrahim na kallon gazarsa ta magana da iyalinsa da ;yan uwansa da ke nesa abu ne marar dadi, kuma zalunci na tsawon shekara guda.

Ya ce "Abubuwa sun kai yanayin da idan wani ya so ya aika sako zuwa ga wani nasa da ke nesa, hanya daya ita ce ka rubuta a takarda ka aika tare da wani da zai je wajen da ake da hanyoyin sadarwa."

Ci gaba da tagayyara jama'a

A yayin da ayyukan jinkai a kasar ta Arewacin Afirka ke daduwa, an mayar da hankali kan kokarin taimakawa fararen hula da aka tsugunar da ke ciki da wajen kasar.

'Yan Sudan da yawa na tuno da rayuwarsu kafin fara yaki. Hoto/GettyImages

Filippo Grandi, Babban KWamishinan Hukumar Kula da "Yan Gudun Hijira ta Mjaalisar Dinkin Duniya, na tsoron tabarbarewar rikicin jinkai da zai iya korar 'yan kasar Sudan har zuwa gaba da kasashe makota inda suka fara zuwa neman mafaka.

Ya ce "Mun san miyagun da ke son amfani da mummunan halin da 'yan gudun hijira suke ciki, da zs su yi kokarin taimaka musu isa ga gabar tekun Arewacin Afirka, ko zuwa Turai."

Iyalai irin su Musa na fatan yakin ba zai dade ba a nan gaba zai zo karshe, domin kr su fara tutananin bazama su shiga duniya su rarrabu.

Abin da muke so kawai shi ne mu koma yin rayuwa mai tsaro, zaman tare, da kwanciyar hankali da muke da ita shekara dayan da ta gabata," in ji Tijjani.

TRT Afrika