A wani abu mai kama da almara da a gasar kofin ƙasashen Afirka ta AFCON 2025 da ake a Maroko, Tanzania ta samu cancantar zuwa zagayen siri-ɗaya-ƙwale, mai ƙasashe 16.
Wannan ne karo na farko da tawagar Tanzania da ake wa laƙabi da “Taifa Stars” ta samu damar kaiwa matakin gaba da na rukuni, tun bayan fara zuwanta gasar shekaru 45 da suka wuce.
A Rukunin C, Tanzania ta ƙare wasan ƙarshe tana matsayi na uku a bayan Nijeriya mai maki 9, wadda ke kan gaba, da kuma Tunisia mai maki 4 da ke matsayi na biyu.
A wasansu na farko, Tanzania ta sha kaye a hannun Nijeriya, sai kuma suka yi canjaras da Uganda da kuma Tunisia, inda suka ƙare da maki 2 kacal.
Kenan Tanzania ba ta yi nasarar cin ko da wasa guda ba. Hasali ma ta yi rashin nasara a wasa ɗaya, saɓanin Mali, wadda ta yi canjaras a duka wasanninta uku, amma ta zo ta biyu a Rukunin A da maki 3.
Fifiko kan Angola
Ko da cewa ba su ci ko wasa ɗaya ba, kuma sun samu maki biyu ne kacal, tawagar ta samu zarcewa zagayen gaba saboda zamowa cikin ƙasashe huɗu masu zarra da suka zo na uku a rukuninsu.
Wani abin lura shi ne Tanzania ta kammala zagayen rukuni da maki iri ɗaya da na Angola, wadda ke ta uku a Rukunin B, wato maki biyu amma ta gaza tsallakewa. Amma bambanci a yawan cin ƙwallo ne ya bai wa Tanzania fifiko.
Ɗanwasan Tanzania, Feisal Salum ya zama jarumi a idon magoya bayan ƙasar, bayan ƙwallon da ya ci Tunisia a minti na 48 wadda ta taimaka musu wafto maki ɗaya daga wasan.
Wannan wata babbar nasara ce ga Tanzania, wadda ke halartar gasar AFCON a karo na huɗu, inda a karon farko ta haura matakin rukuni.
Wani ƙarin abin alfahari ga ‘yan Tanzania shi ne suna cikin ƙasashen da za su karɓi baƙuncin gasar AFCON mai zuwa a shekarar 2027, tare da Kenya da Uganda.














