A lokacin da Asiya Mohammed Sururu ta zama mace ta farko a Kenya da ta cancanci shiga gasar masu nakasa ta ‘Paralympics’ ta 2020 a ƙasar Tokyo, ‘yarwasan wadda ta rasa kafafuwanta biyu ta yi amfani da wannan dama wajen nuna baiwa da ƙwazonta.
A yayin wata hira da aka yi da ita a gidan radiyon gwamnati na Kenya kafin soma gasar wasannin, ta nemi alfarmar masu hada shirye-shirye da su nuna wa ɗaliban makarantu na musamman bidiyon don su kalla.
"Ina son yaran su samu kwarin gwiwa kuma su san cewa komai mai yiwuwa ne,’’ in ji Asiya wacce ta rasa ƙafafunta biyu a wani hatsari da ta yi a lokacin da take da ƙuruciya.
Sai dai ga kowace mace kamar Asiya wadda ta kai matakin wasan Paralympics, da yawan 'yanwasa masu fama da nakasa ba sa kaiwa.
KickStartKenyaFootbal wata ƙungiya da ke rajin haɗa kai a wasannin, ta kiyasta cewa kusan mutane 918,000 - wato kashi 2.2% na yawan jama'a na fama da nakasa.
Da yawa daga cikin mutanen na fuskantar manyan ƙalubale, ciki har da nuna wariya daga al'umma da kuma ƙarancin damammakin samun ilimi da ayyukan yi.
Kenya wadda ta shiga gasar wasannin Paralympic tun a 1972 kuma ta lashe lambobin yabo 49, ciki har dazinare 19, yawancin 'yanwasa masu nakasa daga ƙasar ba su cika kaiwa manyan matakai ba saboda rashin tallafi.
Wani shiri na ƙwallon ƙafa na mata masu nakasa a Nairobi ya samu tallafin kuɗaɗe daga wani attajirin ɗankasuwa kuma mai taimakon jama'a ɗan asalin ƙasar Indiya Saad Kassis-Mohamed don magance waɗannan ƙalubale da ake fuskanta a ɓangare lafiya da matsalolin da ke hana 'yanwasa masu nakasa samun horo da ci gaban da suke buƙata akai-akai.
Tallafin da ake samu ta hanyar WeCare Foundation zuwa ga Cibiyar Wasannin Umoja Adaptive, ya ƙunshi kayayyakin hana samun rauni, da na sufuri da kuma lokutan horarwa akai-akai - a takaice dai abubuwan da ka iya samar da sauki ga ‘yanwasa don fitowa duk mako kuma su samu horo lafiya.
Ga mafi yawan 'yanwasa da ke samun damammakin shirin, ƙalubalen bai tsaya ga samun kwarin gwiwa ba kawai. Amma ga yadda za a iya shawo kan haɗarin rauni da ake yawan samu da kuma maye gurbin kayayyakin da suka tsufa da tabbatar da cewa ba su rasa horo ba.
Ayyukan tallafi
Kassis-Mohamed, wanda aka karrama a shekarar 2025 a matsayin gwarzon Forbes na 'yanƙasa da shekara 30 saboda gudummawar da ya bayar ga al’umma, ya tara dala miliyan 5 ta hanyar Gidauniyarsa ta WeCare don tallafa wa ayyukan da ake gudanarwa a cikin al'ummomin da ba su da isasshen kulawa a faɗin Afirka ta Tsakiya da sauran yankuna.
Ayyukan da yake gudanarwa sun shafi shirye-shirye na sabunta makamashi da tallafin jin kai daga ciki har da aikin amfani da hasaken rana wajen samar da ruwa a Darfur na ƙasar Sudan da kuma shirye-shiryen ci gaban yara a yankin Asiya.
"Muna magana ne kawai game da wasannin masu nakasa idan aka lashe lambobin yabo, amma ba a cika tabo ainihin ayyukan da ke kasa ba," kamar yadda Leila Njoroge, Daraktar Shirye-Shirye a Gidauniyar WeCare, ta shaida wa TRT Afrika.
"Idan ɗan wasa ba zai iya zuwa inda zai samu horo cikin lafiya ba, tare da maye gurbin kayyayyakin da suka lalace, ko kuma ba shi wanda zai duba shi a lokacin da yake cikin ciwo, to tabbas ba zai samu wani ƙwarin gwiwa ba.
Muna son samar da ababen da ake buƙata na yau da kullum wadanda za su bai wa matan ƙarfin gwiwar ci gaba da fitowa filin wasa."
Ƙalubale da dama
Bincike ya nuna cewa 'yan wasa masu nakasa na fuskantar ƙalubale da dama na aiki, tun daga kuɗin sufuri da kayan aiki da ba a tsara su don jikinsu ba da karancin tallafin kiwon lafiya da kuma hanyoyin samun waraka.
Ga mata masu nakasa, galibi waɗannan ƙalubale suna ƙara ta'azzara. A halin yanzu, babu wata ƙungiyar wasanni ta musamman ta ƙasa da ta shafi mata masu nakasa, saboda rashin ƙungiyoyin mata masu alaƙa da nakasa.
Mata na ci gaba da fuskantar ƙarancin damammaki a gasar wasanni ta ƙasa da ƙasa, inda adadin ke kasa sosai a ƙasashe masu tasowa.
Abubuwan da gidauniyar WeCare ke yi sun haɗa da ka'idojin samar da rigakafi idan an ji rauni, da ƙarfafa hanyoyin kariya ga lafiyar 'yanwasa, da lafiyar kwakwalwarsu.
Manufar dai ita ce a tabbatar da cewa ba a katse ba da horo ba ta hanyar taimaka wa 'yanwasa su shawo kan ciwo tare murmurewa cikin sauri don kar a samu wani tsaiko.
"Wasan kwallon ƙafa na mata masu nakasa na bunƙasa, sai dai akwai 'yan wasa da dama waɗanda har yanzu suke fuskantar ƙalubale da ba a cika bayyanasu a labarai ba," in ji Kassis-Mohamed. "Wannan ba tallafi na lokaci ɗaya ba ne kawai; ana buƙatar a ci gaba akai-akai.
Idan 'yanwasa za su iya zuwa samun horo, su motsa jiki lafiya kuma su murmure yadda ya kamata, za a kare hazaka da walwalarsu a lokaci guda."
Ci-gaba da ba da tallafi
Grace Wanjiku, babbar koci a Cibiyar Wasannin Adaptive ta Umoja, ta ce muhimmin abin da za a sa gaba shi yadda za a magance matsalolin da za su iya tasowa cikin sauri.
"Muna da 'yanwasa waɗanda za su iya yin gasa a babban mataki, amma suna fuskatar tsaiko daga waje. Idan aka shawo kan waɗannan ƙalubale, za yi samun horo sosai, sannan za su ji rauni kaɗan kuma za su ci gaba da kasancewa a wasan."
Ƙudaden tallafin da aka samu sun taimaka wajen ƙarfafa shirin, da kuma ci gaba da horo a kan lokaci tare da inganta ƙwarewar ‘yanwasan duk mako wanda ba don haka ba wataƙila da sun daina.










