Yau Litinin, 29 ga Disamba za a fara zagayen ƙarshe na wasannin rukuni a gasar Kofin Afirka ta AFCON 2025 da ke gudana a Maroko.
Ƙasashen da suka tsallaka gaba su ne Nijeriya, Masar, da Aljeriya, yayin da sauran tawagogin suke tararrabin wucewa gaba, musamman Maroko mai masaukin baƙi.
Ƙasashen uku sun lashe wasanni biyu na farko da suka buga a matakin rukuni, wanda ya ba su maki 6 da ya kai su zuwa zagayen ‘yan-16 da za a fara 3 ga Janairun sabuwar shekara.
Wasan ƙarshen matakin rukunin da za a buga, zai tantance tawagogin da za su wuce gaba kai-tsaye, da waɗanda za su zo na uku, wanda daga cikinsu za a zaɓi mafiya yin zarra.
A Rukunin B, Masar ta ci duka wasanninta inda ta samu maki 6 da ya tsallakar da ita gaba. Sai Afirka ta Kudu ta biyu da maki uku. Sai Angola da Zimbabwe masu maki ɗai-ɗai.
Afirka ta Kudu za ta kara da Zimbabwe, sannan Masar ta kece raini da Angola.
Rukunin A na ɗauke da Maroko a saman teburi da maki 4, sai Mali da Zambia masu maki biyu kowannensu, yayin da Comoros ke da maki ɗaya tilo. Maaroko za ta kara da Zambai, sai Mali ta fafata da Comoros.
Ƙasashe uku ba su da maki
A Rukunin C kuwa, Nijeriya, wadda ta riga ta tsallaka gaba da maki 6, za ta kara da Uganda mai maki 1. Ita kuma Tunisia mai maki 3 za ta kara da Tanzania mai maki 1.
Senegal da Congo DR suna da maki 4 kowannensu a Rukunin D, sai Benin mai biye musu da maki 3, yayin da Botswana ke neman samun maki na farko.
Congo DR za ta haɗu da Botswana, sai Benin ta ɓarje gumi da Senegal.
A Rukuni E, Aljeriya ta samu tsallakawa zagayen siri-ɗaya-ƙwale inda za ta kara da Equatorial Guinea, wadda ba ta da maki ko guda.
Sudan da Burkina Faso duka suna da maki uku-uku, kuma za su kara don neman tsira.
Gabon da ba ta da maki a Rukuni F, za ta kara da Ivory Coast da ke saman teburi da maki 4, wadda kuma ita ke riƙe da kofin bara.
Sai ta biyu a rukunin, Kamaru mai maki 4 za ta kara da Mozambique mai 3 ranar Larabar da za a kammala zagayen rukuni na gasar.













