Dakarun Nijeirya da ke kai Farmakan HADIN KAI tare a sabon kaimi sun samu nasara kan ‘yan ta’adda a wurare daban-daban da ke yankunan da ake kai farmakan Hadin Gwiwa a kasar ranar 23 ga Oktoban 2025.
Tsakanin karfe 12 da karfe 4 na dare ‘yan ta’adda sun kai hari ka dakarun soji a Dikwa, Mafa, Gajibo da Katarko, da ke Jihar Borno da Jihar Yobe, in ji sanarwar da jami’in watsa labarai na Farmakan Hadin Kai Laftanal Kanal Sani Uba ya fitar ga manema labarai.
Sanarwar ta ce a dukkan bangarorin, dakaru sun nuna tirjiya tare da fafatawa da jarumta, suka kuma kawar da hare-hare inda suka lallasa ‘yan ta’addar da karkashe su.
Farmakan da sojojin suka kai ta kasa sun samu tallafi ta sama daga Dakarun Sama na Farmakan na OPHK.
Dacewar kai farmakan, tare da fahimtar inda aka dosa a filin daga da Sashen Leken Asiri ya bayar, sanya idanu da kayan aiki ne suka ba wa dakarun damar mayar da martani a kan kari tare da cin nasara, in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma ce “Gamayyar kokari ta sama da ta kasa ya kai ga kassara sama da ‘yan ta’adda 50 a dukkan yankunan.
Dakarun sun kuma kwato bindigu samfurin Ak-47 guda 38, PKT guda 7, RPG guda 5GPMG guda 2 da gurnetin hannu da kuma dubunna harsashai. Haka zalika dakarun ta kasa da ta sama na ci gaba da bin ‘yan ta’adda sama da 70 da suka samu raunuka.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa bayanan sirri sun bayyana cewa ‘yan ta’addar da suka kai hare-hare Dikwa da Gajibo sun sulalo ne daga bangaren Kamaru, yayin da wadanda suka kai hari Katarko kuma suka fito daga yankin Timbuktu, sanannen wajen da ‘yan ta’adda ke zama.
“Wasu daga dakarun soji sun samu raunuka a filin daga amma suna cikin yanayi mai kyau. Wuta ta kama wasu gine-gine da da ababan hawa sakamakon hari daga drone da RPG a lokacin fadan musamman a Mafa da Dikwa…”
Babban Ofishin Sojojin ya yaba wa sadaukantaka da jarumtar dakarun. Jajircewarsu ta sake bayyana sojojin a shirye suke kuma suna da ikon kare kasar da iyakokinta daga duk wata barazana, in ji sanarwar.










