Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta sanar da kuɗin Aikin Hajji na shekara mai zuwa ta 2026 da aka ƙayyade kan naira miliyan 8.1, miliyan 8.2 da miliyan 8.5.
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ne ya sanar da hakan bayan rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi da kamfanonin da ke tafiyar da hidimomin alhazai a ƙasar Saudiyya.
Wata sanarwa daga sashen yaɗa labarai na hukumar ya fitar ta ce: “Bayan tuntubar duka masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabannin jihohi da samun amincewar Gwamnatin Tarayya da Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya sanar da kuɗin Hajjin 2026 kamar haka:
– Yankin Maiduguri–Yola (Yobe, Borno, Adamawa da Taraba) za su biya N8,118,333.67.
– Sauran jihohin Arewa za su biya N8,244,813.67.
– Jihohin Kudancin ƙasar za su biya N8,561,013.67.
Idan aka kwatanta da abin da aka biya bara, a bana kowane maniyyaci zai samu ragin aƙalla naira 200,000.”
Wakilan Hukumar NAHCON da a halin yanzu suke a Saudiyya sun gana tare da sanya hannu kan yarjejeniya da kamfanin da zai yi hidimar alhazai a shekarar 2026 wato kamfanin Mashareeq Al-Zahabiyya da kuma kamfanin sufuri na Daleel Al-Ma’aleem.
Farfesa Usman ya ja hankalin duk masu niyyar zuwa Aikin Hajji su kammala biyan kuɗin su kafin 31 ga Disamba 2025.