Kakakin Majalisar Wakilai na Nijeriya Dakta Abbas Tajudeen, ya ce majalisar na tare da Shugaba Tinubu ɗari bisa ɗari a shirinsa na karɓar bashi.
Yayin gabatar da jawabin buɗe taro a taron shekara-shekara na 8 na African Network of Parliamentary Budget Offices Conference, Dokta Tajudeen ya bayyana cewa an yi kuskuren fassara matsayar Majalisar a kan batun gwamnati na karɓar bashi a baya-bayan nan.
Kakakin ya bayyana haka ne a yayin wani taro karo na takwas na ofisoshin kasafin kuɗi na majalisun Afirka inda ya bayyana cewa ana yi wa matsayar majalisa mummunar fahimta dangane da batun cin bashi.
A cewarsa, shirin gwamnati na karɓar bashi a yanzu wani yunƙuri ne na farfaɗo da tattalin arziki tare da tallafa wa manyan ayyuka masu muhimmanci.
Ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa duk wani bashi da za a karɓa a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Tinubu za a karɓe shi cikin gaskiya, ɗorewa, kuma daidai da tsarin bashi na matsakaicin lokaci na Nijeriya da kuma bin ƙa’idojin duniya.
“A baya-bayan nan, wani jawabi da shugaban masu rinjaye a majalisa ya yi a taron Majalisun Yammacin Afirka an ruwaito shi cikin kuskure da mugunta, wanda ya sa aka samu mummunar fahimtar cewa Majalisar Wakilai ba ta goyi bayan shirin karɓar bashi na gwamnatin Tinubu ba. Dole mu fayyace cewa wannan fahimta ba daidai ba ce kuma tana yaudarar jama’a.”
Ya kuma bayyana cewa nahiyar Afirka gaba ɗaya tana rasa fiye da dala biliyan 587 a duk shekara sakamakon rashawa, haramtattun kuɗaɗe da kuma rashin ingancin gudanarwa.
Kakakin majalisar ya ƙara da cewa Nijeriya na rasa kimanin dala biliyan 18 a kowace shekara saboda laifukan kuɗi, abin da ya kai kashi 3.8% na ma’unin GDP na ƙasar. Ya jaddada buƙatar ƙarfafa ikon sa ido na kuɗi da majalisu ke da shi don kare dukiyar jama’a.