A ranar Litinin ne ake fara Babban Taron Majakisar Dinkin Duniya wato UNGA a birnin New York na Amurka.
Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima ne ya jagoranci tawagar ƙasar don halartar taron karo na 80 da za a yi daga ranar Litinin 22 zuwa Lahadi 28 ga watan Satumban 2025.
Ga dai abubuwan da tawagar Nijeriyar za ta gudanar a taron:
Taruka
Kashim Shettima, wanda zai wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da jawabin Nijeriya a babban taron na duniya, sannan zai shiga cikin wasu muhawarori da za a gudanar kan al’amura da dama na duniya.
Sannan zai yi ƙananan taruka da jami’an diflomasiyya da dama a gefen babban taron.
Yayin kasancewarsa a birnin New York, Mataimakin Shugaban Ƙasar zai sanar da sabbin gudunmawa na ƙasa da ƙasa a karkashin Yarjejeniyar Paris da kuma halartar babban taron tattaunawa kan samar isassun gidaje masu araha.
Muradu
Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar ya jaddada aniyar ƙasar ta samar da ingantacciyar alaka tsakanin bangarori da dama da kuma inganta hulɗar ƙawance.
Da yake magana game da burin Nijeriya na taron UNGA na bana, Ministan Harkokin Waje, Ambasada Tuggar, ya ce Nijeriya tana jagorantar shirin Majalisar Dinkin Duniya kan haraji a duniya, wanda ke da matukar muhimmanci ga yunkurin da ake yi na sake fasalin tsarin hada-hadar kuɗaɗe na duniya.
Ya ce, “Wannan wani abu ne da ya sanya Nijeriya a matsayi na shugabanci, kuma za ka ga a yayin taron ganawa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, akwai Ministoci da manyan jami’an gwamnati, kuma duk dalilin yin wannan bayanin shi ne domin mu kasance tare da juna.
Ministan ya yi nuni da cewa, Afirka ita ce nahiya ko kungiya daya tilo da ke da matsaya daya kan abin da ya kamata a yi wajen yin garambawul a kwamitin sulhu na MDD, yana mai jaddada cewa Afirka ta samu mafi karancin kujeru biyu na din-din-din bisa abin da ake kira Yarjejeniyar Ezulwini da kuma sanarwar Sirte.
“Muna kuma da batun wanzar da zaman lafiya, ka san Nijeriya ta shiga daya daga cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya 60 da Majalisar Dinkin Duniya ta yi, muna so mu tabbatar da cewa idan ana maganar zaman lafiya, gudunmawar da ake bayarwa wajen wanzar da zaman lafiya, ba ta sojoji ba ce kadai, har ma da ta kudade.
"Nijeriya na ba da gudunmawa ba kawai a bangaren Afirka ba, har ma a bangaren Majalisar Dinkin Duniya, mun sake jaddada matsayin Nijeriya kan rikicin Gabas ta Tsakiya, a Gaza, Falasdinu, da batun gabashin Kongo, da rikicin Sudan.
“Mataimakin Shugaban Ƙasar zai gana da Firaministan Sudan, kuma zai halarci taron kwamitin sulhu da tsaro na Tarayyar Afirka," in ji shi.
Tawaga
Tawagar Nijeriya a Taron UNGA ta haɗa da Ministan Harkokin Wajen Ƙasar, Yusuf Maitama Tuggar, da Ministan Tsaro Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, da Jakadan Nijeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Ambasada Samson Itegboje.
Sannan akwai Ministan Ƙirƙire-Ƙirƙire da Kmiyya da Fasaha, Chif Uche Nnaji, Jakadan Tsaron na Nijeriya a New York, Birgediya Janar Edward Koleoso da Jakadan Tsaro na Nijeriya a Washington, Group Captain Sani Kalgo, da sauransu.
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya ce halartar UNGA karo na 80 da Nijeriya ke yi zai sake sanya ƙasar a wani matsayi na zuwa a zuba jari da kuma zama ɗaya dsaga cikin ƙsashen Afirka mafiya ƙrfin tattalin arziki.