Masu amfani da shafukan sada zumunta a Nijeriya sun shafe ƙarshen mako suna muhawara kan digirin girmamawar da wata jami’a mai suna European-American University ta bai wa shahararren mawaƙin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara.
Bidiyon da ke nuna yadda ake karrama Rarara da digirin girmamawar ya karaɗe kafafen sada zumunta a ƙarshen mako.
Sai dai cikin wani saƙo da ta fitar a shafinta a ranar Asabar, jami’ar ta ce sam ba ta da hannu a lamarin kuma ba da izininta aka ba shi ba.
Wannan batu ya jawo muhawara daga wajen ‘yan boko da sauran al’umma kan dacewa ko rashin dacewar bai wa Rarara digirin girmamawa na dokta.
Yanzu za mu yi nazari ne a kan kalmar Dokta da rabe-rabenta da bambance-bambancen da ke tsakaninsu.
Dokta da ake sanyawa a farkon suna ya kasu kaso biyu ne wato na makaranta ko ilimi da kuma na girmamawa wanda ake ba mutum ko da bai taba yin jami’a ba.
Kuma ana bayar da shi ne saboda wata muhimmiyar gudunmawa, kamar yadda tsohon Registrar a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria Dokta Aliyu Dalha Kankia ya shaida mana.
Dr Aliyu Kankia ya ce Doktan karatu a makaranta ya kasu kashi biyu ne. Ya ce akwai wanda ake kiran wadanda suka karanci aikin likitanci wato Medicine da kuma karatun likitan dabbobi wato Veterinary Medicine.
Tsohon babban jami’in na ABU ya ce duk wani ɗalibi da ya gama karatun kimanin shekara shida a wadannan fannuka biyu ana kiransa Dokta.
Bayan wannan akwai Dokta na PhD wanda bayan mutum ya kammala digiri na uku a jami’a yake samu. Dokta Aliyu Kankia ya ce mutum yana samun digiri na uku (Dokta) ne daga jami’a bayan ya kammala digirin farko da kuma digiri na biyu wato Masters.
Masu neman Dokta na karatu (PhD) sukan kwashe tsawon shekaru masu yawa wasu har fiye da shekara 10 wajen neman digiri na uku musamman a jami’o’in Nijeriya. Ana cin kwakwa matuƙa gaya a wajen kai wa irin wannan matsayi na Doktan Phd, saboda yakan haɗa da bincike da rubuce-rubucen maƙaloli.
Misalin waɗanda suka samu Dokta (PhD) na karatu a baya-bayan nan shi ne Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II da kuma shahararren lauyan nan dan Nijeriya mazaunin Birtaniya wato Barista Bulama Bukarti.
Sannan Dokta Aliyu ya ce akwai Dokta Honoris Causa wanda shi ne digirin girmamawa wanda jami’o’i suke bayarwa ga mutanen da suka nuna hazaƙa ko basira kan wani fanni na rayuwa ko sana’a ko kuma wanda mutum ya yi jan aiki ci gaban al’umma da dai sauransu.
Irin wannan digiri a kan ba da shi har ga waɗanda ba su yi karatun boko ba idan dai har sun ba da muhimmiyar gudunmawa wajen gina al’umma, ko da kuwa mawaƙa ne ko ‘yan kasuwa ko wani rukunin mutane.
Misalin irin wannan shi ne Marigayi Dokta Mamman Shata Katsina, wanda yana cikin fitattun mutanen da suka taɓa samun irin wannan digirin girmamawa daga Jami’ar Ahmadu Bello Zaria.
Sannan akwai wasu mawaƙan irin (Dr) Ɗanmaraya Jos (Dr) Aliyu Namangi (Dr) Ali Akilu da su ma suka taba samun irin wannan digirin girmamawa na zama dokta.
Kazalika Farfesa Abdullah Uba Adamu, a wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta Alkalanci, ya ce akwai ma Doktan da ake saye da kuɗi haka siddan, kuma an fi sayen irin wannan digirin girmamawar a jami’o’in da ke yankin Carribean.
Dokta Aliyu Kankia ya ce a baya ana bambanta Doktan Karatu da Doktan Digirin Girmamawa, ya ce Dr da ake sanyawa a farkon suna yana nufin na karatu ke nan yayin da wanda (Dr) da ake sakawa a cikin baka yana nufin wanda ya samu nasa Doktan daga digirin girmamawar da aka ba shi ke nan.
Sai dai ya ce a yanzu akwai wasu masu digiri na uku (na karatu) da ke sanya PhD a karshen sunansu don su bambanta kansu daga masu digirin girmamawa da suke sanya Dokta a farkon sunansu ba tare da sakawa a () ba.
Tsohon Registrar na ABU ya ce duk cikin wadannan digirin na’uka uku, digirin girmamawa shi ne ya fi jawo ce-ce-ku-ce da ruɗani saboda yadda ya ce wasu jami’o’i suke bayar da shi barkatai.
Ya ce wasu jami’o’i suna bayar da shi ne saboda kwadayin abin da za su karba, ko alfarma daga wurin wanda suka baiwa.
A cewarsa, saboda haka ne aka yi doka a Nijeriya wacce ta hana bai wa mutum digirin girmamawa idan har yana rike da mukamin gwamnati ko siyasa, har sai bayan mutum ya sauka daga muƙami.