NIJERIYA
2 minti karatu
Sassa daban-daban na Jihar Kaduna na cikin duhu sakamakon faɗuwar turken dakon lantarki
Faɗuwar ta faru ne sakamakon ruwan sama mai yawa da iska mai karfi, inda kuma ayyukan masu lalata turakun suka bayar da gudunmawa, inda aka gano cewa an cire muhimman sassan turken.
Sassa daban-daban na Jihar Kaduna na cikin duhu sakamakon faɗuwar turken dakon lantarki
TCN ya ce tawagar injiniyoyinsa ta isa wajen da lamarin ya faru domin sake kafa wani sabon turken da ya faɗi. / Others
6 awanni baya

Sassa daban-daban na Jihar Kaduna da ke arewacin Nijeriya na cikin duhu sakamakon faɗuwar wani turken da ke dakon lantarki, kamar yadda kamfanin da ke dakon wutar lantarki na Nijeriya TCN ya tabbatar.

Mai magana da yawun TCN, Ndidi Mbah, ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a turke mai lamba 7 da ke kai wa Kaduna wuta a yankin Rigasa na Karamar Hukumar Igabi.

Faɗuwar ta faru ne sakamakon ruwan sama mai yawa da iska mai karfi, inda kuma ayyukan masu lalata turakun suka bayar da gudunmawa, inda aka gano cewa an cire muhimman sassan turken.

Sakamakon haka, sassa daban-daban musamman na kudancin jihar sun rasa lantarki, inda lamarin ya shafi gidajen jama’a da masana’antu.

“Faɗuwar turken ya jawo katsewar wutar lantarki zuwa wasu cibiyoyin rarraba wutar lantarki na Kaduna Electric, musamman waɗanda ke bayar da wuta ga Kudancin Kaduna,” in ji sanarwar.

 “Yayin da suke duba wurin da lamarin ya faru, ma’aikatan TCN sun gano cewa wasu ɓarayi sun sace wasu sassan turken, wanda hakan ya sa ya yi sauƙin faɗuwa.”

“Duk da haka, don rage illar wannan matsala, TCN ta shawarci kamfanin Kaduna Electric Distribution Company da ya haɗe layin wutar 33kV Mogadishu da 33kV Abakwa, domin bai wa kwastomomin Mogadishu damar samun wutar lantarki.”

Sai dai TCN ya bayyana cewa sauran sassan Kaduna, ciki har da Kinkinau, Yan Tukwane, Kabala West, Unguwan Mu’azu, da Kaduna North, ba su shiga cikin matsalar ba.

Haka kuma, TCN ya ce tawagar injiniyoyinsa ta isa wajen da lamarin ya faru domin sake kafa wani sabon turken da ya faɗi.