NIJERIYA
2 minti karatu
Boko Haram: Sojojin Saman Nijeriya sun kashe 'yan ta'adda fiye da 25 a Borno da Yobe
Mai magana da yawun Rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce jiragen yaƙinsu sun kai samamen ne ranar 18 ga watan Satumba bayan sun samu bayanan sirri daga sojojin ƙasa.
Boko Haram: Sojojin Saman Nijeriya sun kashe 'yan ta'adda fiye da 25 a Borno da Yobe
Kakakin rundunar sojin saman Nijeriya Ejodame ya ce jiragen yaƙinsu sun kai samamen ne bayan sun samu bayanan sirri daga sojojin ƙasa / Reuters
20 Satumba 2025

Sojojin Saman Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda fiye da 25 a wani samame da suka kai da cikin dare a yankin Bula na Jihar Yobe da Banki a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Mai magana da yawun Rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame, shi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Ejodame ya ce jiragen yaƙinsu sun kai samamen ne ranar 18 ga watan Satumba bayan sun samu bayanan sirri daga sojojin ƙasa.


Ya ƙara da cewa masu tattara bayanan sirri sun bi diddigin yadda rukunonin ‘yan ta’adda suke kai komo sannan suka miƙa bayanan ga sojojin sama inda nan-take suka yi musu luguden wuta a arewacin Banki.


“Jiragen yaƙin sun kai samame uku a kan ‘yan ta’adda a yayin da suke kai komo da kuma lokacin da suka taru a maɓoyarsu, inda suka kashe mayaƙa fiye da 25,” in ji Air Commodore Ejodame.


Ya ƙara da cewa: “Bayan kammala kai samamen, dakarun sojin ƙasa sun tsaya cikin shirin ko-ta-kwana amma babu wata barazana da suka fuskanta ta hari.”

Dakarun Nijeriya sun samu wannan nasara ce a yayin da ‘yan ta’adda suke ƙara ƙaimi wurin kai hare-hare a arewa maso gabashin ƙasar.

A farkon watan Satumba, mayaƙan Boko Haram sun kai hari Dar-El-Jamal da ke ƙaramar hukumar Bama inda suka kashe aƙalla mutum 63.