NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamnatin Nijeriya ta damu kan bidiyon tallan bogi na Tinubu da aka yi da Ƙirƙirarriyar Basira
Wannan sanarwa ce ga jama’a don su ankara game da wani talla na bogi da aka tsara da ƙirƙirarriyar basira inda aka yi amfani da hoto da bidiyon shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu wajen neman saka jari a shirin kasuwanci na damfara, in ji sanarwar.
Gwamnatin Nijeriya ta damu kan bidiyon tallan bogi na Tinubu da aka yi da Ƙirƙirarriyar Basira
Shugaba Tinubu bai san da tallan na boge ba, in ji hukumar ARCON / Reuters
25 Satumba 2025

Gwamnatin Nijeriya ta yi gargaɗi game da amfani da tallan bidiyon bogi na Shugaba Bola Tinubu da aka haɗa da ƙirƙirarriyar basira wanda ke yawo a shafin sada zumunta na Facebook.

Ta bayyana cewa tallan, wanda ya yi iƙirarin tallata neman zuba jari a wani shiri na damfara mai samar da riba mai yawa cikin sauri, ba shugaban ƙasa ko hukumar da ke sa ido kan tallace-tallace ta Nijeriya (ARCON) ce ta ba da izinin yin sa ba.

ARCON wata hukuma ce da ke ƙarƙashin ma’aikatar watsa labarai da wayar da kan jama’a ta Nijeriya.

Wata sanarwa da babban darakatan hukumar ARCON, Dakta Olalekan Fadolapo, ya fitar ta bayyana hatsarin yaɗa labaran ƙarya inda ta ce: “Wannan sanarwa ce ga jama’a don su ankara game da wani talla na bogi da aka tsara da ƙirƙirarriyar basira inda aka yi amfani da hoto da bidiyon shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu wajen neman saka jari a shirin kasuwanci na damfara.”

Yayin da take kira ga masu kafafan watsa labarai da ma jama’a bakiɗaya su yi  taƙatsantsan, gwamnatin ta bayyana cewa:  “Taka tanade-tanaden doka ta 23 ta shekarar 2022 zai janyo tuhuma.”

ARCON ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa ba a miƙa tallan domin tantancewa ba kuma hukumar ba ta bayar da izinin wallafa shi ba.

Hukumar ta jaddada jajircewarta wajen samar da wani yanayi na talla mai ɗa’a da kuma kare masu kallon talla, tana mai kira ga masu ruwa da tsaki su ɗabbaka ƙa’idodin tallace-tallace na martaba gaskiya da tsafta.